Ka da ku sake ku nemi mulki a 2023 – IYC, Afenifere ga ‘Yan Arewa

Ka da ku sake ku nemi mulki a 2023 – IYC, Afenifere ga ‘Yan Arewa

Shugabannin mutanen yankin Kudancin Najeriya da kungiyoyin shiyyar, sun gargadi mutanen Arewa cewa ka da su fito neman takarar shugaban kasa a zaben 2023 domin hadin-kan kasar.

Kungiyoyin Kudu irinsu "Ohanaeze Ndigbo" ta Ibo da kuma kungiyar Afenifere mai kare hakkin Yarbawa da Takwararta ta Neja-Delta watau "Ijaw Youth Congress" sun fara magana a kan 2023.

A wasu mabanbantan hira da kungiyoyin su ka yi Jaridar Saturday Tribune, sun ja-kunnen ‘Yan siyasan Arewa a kan yunkurin ganin sun gaji shugaba Muhammadu Buhari a kan mulkin kasar.

Wadannan kungiyoyi sun bayyana cewa kokarin Arewa ta cigaba da rike mulki ya na da matsala a kasar. Sai dai wasu kungiyoyin Arewar su na gani babu komai don mulki ya tsaya a yankin.

KU KARANTA: 2023: Komai bakin-cikin tanda sai an ci waina - Adeboye kan Osinbajo

Babbar kungiyar nan ta Arewa Consultative Forum da kuma Takwararta a yankin watau Coalition of Northern Groups sun ce sam babu wani abu da wani ‘Dan Arewa ya gaji Muhammadu Buhari.

Ijaw Youths Council ta na ganin idan mulki ya cigaba da zama a Arewa, an sabawa kama-kaman da aka saba tsakanin Kudu da Arewa wanda hakan babbun hadari ne ga kasar da kuma siyasarta.

Shugaban kungiyar ta IYC, Pereotubo Oweilaemi, ya ce za a taka sauran bangarorin kasar idan shugaban kasa ya kuma zama ‘Dan Arewa. A ganinsa zai yiwu Arewa ta cigaba da rike kasar.

A 2023, zai kasance shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas a kan mulki. Wannan zai sa ‘yan siyasar Kudu maso Yamma ko Gabashin kasar su nemi a ba su na su daman.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel