Dalilin da yasa Marafa da sauran ‘yan G-8 ke goyon bayana – Gwamna Matawalle

Dalilin da yasa Marafa da sauran ‘yan G-8 ke goyon bayana – Gwamna Matawalle

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara a jiya Litinin 7 ga watan Oktoba, 2019 ya ce ya zama wajibi ga Sanata Kabiru Marafa tare da ‘yan kungiyarsa dake karkashin jam’iyyar APC wato ‘yan G-8 su goya masa baya domin cigaban jiharsu.

Daily Trust ta tattaro mana bayanan cewa karar da Kabiru Marafa ya shigar da jam’iyyarsa ta APC ce dalilin day a sanya a kori zaben jam’iyyar kasancewar na a gudanar da zaben firamare ba.

KU KARANTA:Yawan ‘yan Najeriya cikas ne ga cigaban kasar – Sarkin Kano

Wannan dalilin ne ya sanya kotun koli tayi watsi da kuri’un jam’iyyar APC a zabukan da aka gudanar gaba daya na shekarar nan. Tare da Marafa akwai wasu jiga-jigan jam’iyyar APC su bakwai.

Matawalle da yake karbar bakuncin Marafa tare da mutanensa a fadar gwamnatin Gusau ya ce: “Idan har na gaza wurin aiwatar da ayyukana, bani kadai na gaza ba kune ‘yan G-8 kuka gaza. A don haka ya zama wajibi ku bani goyon baya domin daga martabar jiharmu. Ku zo muyi aiki tare, gwamnatinu ta kowa da kowa ce.”

Ya yi mika godiyarsa ga Marafa a kan irin goyon baya da kuma addu’o’in da yake yi masa tare da mabiyansa. Gwamnan ya kara da cewa a shirye yake da bin doka da oda yayin gudanar da mulkinsa.

Matawalle ya ce: “Gwamnatinmu babu ruwanta da jam’iyya. Manufarmu kawai ita ce cigaban jiharmu ta Zamfara. Ba zan kira da suna ‘yan APC ba sai dai in kira ku da suna masoya cigaban jihar Zamfara. Kamar yadda kuka fadi Allah ne ya zabe ni tabbas wannan magana gaskiya ce, kuma yiwa jiharmu aiki shi ne kan gaba a mulkinmu.”

https://www.dailytrust.com.ng/why-marafa-others-must-support-me-matawalle.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel