Atiku da Saraki sun yi magana game da lalata da ake a Jami’o’in Afrika

Atiku da Saraki sun yi magana game da lalata da ake a Jami’o’in Afrika

A cikin ‘yan kwanakin nan ne Jaridar BBC Hausa ta fito da wani rahoto na binciken kwa-kwaf din da ta yi a game da yadda Malaman jami’o’i ke amfani da ‘Yan makaranta a fadin Nahiyar Afrika.

Tuni jama’a da da-dama su ka fara tofa albarkacin bakinsu a kan wannan bincike inda har tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ‘dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ya yi magana.

Alhaji Atiku Abubakar ya fito ya yi kira da a kawo karshen ta’adin da Malaman jami’o’i su ke yi na amfani da ‘Dalibansu a Najeriya da ma sauran kasashen Afrika da abin ya yi mugun kamari.

A wasu jerin sakonni da Atiku Abubakar ya fitar a shafinsa na Tuwita jiya Litinin, 7 ga Watan Oktoba, 2019, ya yi tir da abin da ke faruwa tare da yin kira a kawo hanyar maganace matsalar.

Atiku Abubakar ya rubuta: “Yanzu nan na karanta labarin #SexForGrades (yadda ake kwanciya da ‘Dalibai domin a ci jarrabawa) a jami’o’in kasashe da-dama na Yankin Afrika ta Yamma.”

KU KARANTA: Abin da ya faru da daya daga cikin Malaman jami'an da aka tonawa asiri

Hakan abin Allah-wadai ne da yake bukatar a kawo dabarun da za a kawo karshen wannnan dabi’a.” Atiku ya na maida martani ne kan labarin wani Malami ne mai suna Boniface Igbeneghu.

Shi ma tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma majalisa ta sake duba kudirin haramta lalata da ‘yan makaranta.

A lokacin da Saraki ya ke majalisa, ya kawo wani kudiri da ya yankewa Malaman da ke kwanciya da ‘Dalibansu hukuncin daurin shekaru 5. Saraki ya ce ya kamata a sake kakkabo wannan kudiri.

A matsayina na Uba, na girgiza da barnar wasu Malamai da aka bankado a binciken #SexForGrades. Bai kamata mu bar wannan mummunan hali ya cigaba da yaduwa ba.” Inji Saraki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel