Ina nan da raina ban mutu ba - Fakhriyya ta fito ta karyata maganar mutuwarta

Ina nan da raina ban mutu ba - Fakhriyya ta fito ta karyata maganar mutuwarta

- Wata budurwa 'yar Najeriya mai suna Fakhriyya Hashim ta tashi ta samu wani labari mai rikitarwa

- Yayin da ta samu ko ina a kafafen sadarwa ana wallafa hotonta da katin gayyata na daurin aure sannan ana rubuta cewa ta mutu a kasa

- Budurwar ta bayyana cewa tana nan da ranta ba ta mutu ba, wasu ne dai ke son ganin ta mutu

Wata budurwa mai suna Fakhriyya Hashim ta tashi ta iske wani labari mai rikitarwa a rayuwarta, inda ta samu ko ina a kafafen sadarwa ana wallafa cewa ta mutu.

Mutane da yawa sun wallafa hotunan Fakhriyya tare da wani katin gayyata, inda ake bayyana cewa ta mutu ranar Juma'ar nan da ta gabata 4 ga watan Oktobar nan, inda suka bayyana cewa ta mutu ne awanni kadan a daura mata aure ranar Asabar 5 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Tashin hankali: Yadda sama da maza 500 suka yi mini fyade - Wata budurwa tayi bayani

Da take mayar da martani akan wannan labarin kanzon kurege dake yawo a kafar sadarwa, Fakhriyya ta ce:

"Na jima bana yin Facebook, amma naga wani labarin karya da yake yawo.

"Hotona yana ta yawo a shafukan sadarwa da sunan wata wai Fatima Yola, inda aka bayyana cewa wai za'a daura mini aure yau Asabar amma na mutu ranar Juma'a.

"Mutane na son suyi amfani da hoto na su samu, ku kuma kun dauka kun yafa kuna yadawa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel