Tashin hankali: Yadda sama da maza 500 suka yi mini fyade - Wata budurwa tayi bayani

Tashin hankali: Yadda sama da maza 500 suka yi mini fyade - Wata budurwa tayi bayani

- Wata budurwa 'yar kasar Birtaniya ta bayyana irin halin da ta shiga a lokacin da take yarinya

- Ta bayyana cewa sai da sama da mutane 500 suka yi mata fyade kuma babu abinda aka yi a kai

- Ta ce a lokacin tana ganin hanya daya ce mafita a gareta shine ta mutu, saboda ta kai rahoto wajen 'yan sanda sunki daukar mataki

A karo na farko wata mata tayi magana akan yadda aka yi mata fyade sama da sau dari biyar a cikin shekara bakwai, da kuma yadda 'yan sanda suka yi watsi da maganar ba tare da sun dauki mataki ba.

Da take bayani, matar mai suna Jennifer, wacce a yanzu haka take da shekara 40, ta ce an kama ta a lokuta da dama da laifin karuwanci, inda a lokacin da ta cika shekara 19 tana da laifi 52.

Ta ce wasu mutane ne suka kai mata hari a Telford dake Shropshire, inda a tarihi aka bayyana abinda aka yi mata a matsayin cin zarafi mafi girma a kasar Birtaniya.

Jennifer ta ce tana 'yar shekara 11 a lokacin da aka fara kai ta wajen mutumin da ya fara yi mata fyade. Daga nan suka kira abokanan su suka yi mata fyade, ta bayyanawa jaridar Sunday Mirror cewa tana da shaidar da za ta bayar na cewa lamarin ya faru.

KU KARANTA: Ke duniya: An kama matasa guda biyu da suka yi lalata da gawar wata mata mai shekara 84 a duniya

Ta bayyana cewa ana bata kwaya ta sha sannan suyi mata fyade. Jennifer ta kara da cewa a kowanne dare kimanin mutane 10 ne ke zuwa yi mata fyade.

Ta ce: "A lokacin ina ganin kawai hanya daya ce mafita a gareni shine kawai na mutu, saboda na kaiwa 'yan sanda rahoton abinda ake yi mini sunki daukar mataki."

Ta ce maimakon abin yayi sauki sai gaba da ya kara yi ma, domin kuwa wani tsohon mutumine ya dauketa ya dinga yawo da ita a cikin kasar yana bawa baki suna yi mata fyade.

Ta ce: "Har kulle ni yayi na tsawon kwanaki uku a cikin wani daki, kuma an kaiwa 'yan sanda rahoton cewa an sace ni amma babu abinda suka yi."

A karshe dai an kama shi, amma kuma bayan ya fito sai ya zo har gida da bindiga yake yi mata barazanar kisa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel