Ke duniya: An kama matasa guda biyu da suka yi lalata da gawar wata mata mai shekara 84 a duniya

Ke duniya: An kama matasa guda biyu da suka yi lalata da gawar wata mata mai shekara 84 a duniya

- An kama wasu yara matasa guda biyu da suka je har kabarin wata tsohuwa suka tono suka yi lalata da ita

- Wannan lamari dai ya faru a kasar Philippine ne, inda aka kama matasan bayan wasu da lamarin ya faru a gaban su sun tona musu asiri

- Yanzu haka dai yaran sun shiga hannu, sai dai kuma duka sun musanta zargin da ake yi musu

An kama wasu matasa guda biyu, bayan sun tone kabarin wata tsohuwar mata mai shekaru 84 inda suka yi lalata da ita.

Matasan da ba a bayyana sunan su ba, an kama su ne bayan 'yan uwan matar sun kai ziyara kabarin ta kwana daya bayan an binne ta a ranar 29 ga watan Satumbar nan a garin Davao dake kasar Philippines.

A yadda jaridar Mail Online ta ruwaito, sun gano cewa an tone kabarin matar mai suna Isabel Bastatas, sannan kuma sun gano cewa kamar an fito da ita daga cikin akwatin da aka sanya ta anyi lalata da ita.

Rundunar 'yan sanda ta garin Digos sun bayyana cewa suna gabatar da bincike akan wannan lamari na cin zarafin gawar matar da aka zo har makabarta aka yi.

KU KARANTA: Bayan shafe lokaci mai tsawo ba aji duriyarta ba, tsohuwar jaruma Farida Jalal ta dawo shirin fim

Shugaban rundunar 'yan sandan, Lieutenan Colonel Ernesto Castillo ya ce: "Sun samu nasarar kama matasan ne bayan wasu wadanda aka yi abin a gabansu sun zo sun bayyana musu gaskiyar lamarin.

"Sun bayyana sunan daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna 'Erwin' da kuma wani abokin shi."

Bayan an gano cewa wadanda suka aikata wannan abu yarana ne matasa, an kai su wajen wata hukuma, inda kuma duka suka musanta aikata wannan abu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel