Lalata da dalibai don maki: Bidiyon malamin jami'a yana kuka a aji bayan da dalibai su kayi masa ihu

Lalata da dalibai don maki: Bidiyon malamin jami'a yana kuka a aji bayan da dalibai su kayi masa ihu

An dauka hoton bidiyon Farfesa Gyampo, malami a jami'ar Ghana da aka yi wa tonon silili a cikin bidiyon binciken kwafkwaf da BBC Africa Eye tayi yana kuka a gaban dalibansa bayan fitowar bidiyon.

An dai haska Farfesa Ransford Gyampo wadda malami ne a tsangayar kimiyyan siyasa na jami'ar Ghana yana neman fara soyaya da wata 'yar jarida da tayi badda kama a matsayin daliba a bidiyon na 'S*x for grades'.

A cikin bidiyon, an gano Farfesa Gyampo yana fadawa 'yar jaridar da tayi badda kama cewa yana son ya aure ta kuma ya taimaka mata bayan ta nuna cewa tana son cigaba da karatu a tsagayar da ya ke koyarwa kuma a fanin da ya kware.

DUBA WANNAN: An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

'Yan makonni kadan bayan haduwarsu, Farfesan ya nemi ya ziyarci 'yar jaridan da tayi badda kama a matsayin daliba da ke son yin karatu a karkashinsa a gidan ta amma sai ta ce su hadu a wani kanti.

An nuna farfesan yana ta furta kalaman da ba su dace ba gareta inda ya ce zai aure ta kuma ya nemi ta bashi izini ya sumbace ta amma ba ta amince ba.

Bayan fitowar bidiyon, an ruwaito cewar Farfesa Gyampo ya tafi aji domin koyar da dalibansa amma zai ya fara zubar da hawaye bayan daliban sun yi masa ihu.

Ga dai bidiyon a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel