Nima an nemi yin lalata da ni a yayin da na ke jami'a, inji matar gwamna Fayemi

Nima an nemi yin lalata da ni a yayin da na ke jami'a, inji matar gwamna Fayemi

- Matar gwamnan jihar Ekiti, Ereku Bisi Fayemi ta ce tayi magana kan batun neman lalata da malaman jami'o'i keyi da dalibai don basu maki

- Bisi Fayemi ta ce ita kanta abin ya faru da ita a lokacin da ta ke matashiya a jami'a amman wadanda ke neman cin zarafin nata ba su kai ga cin nasara ba

- Uwargidan gwamnan ta shawarci mata su rika tona asirin masu neman cin zarafinsu kuma tayi alkawarin kungiyar matan gwamnoni za ta dauki mataki kan lamarin

Bayan fitowar binciken kwakwaf da BBC ta gudanar kan yadda malaman jami'ar ke neman yin lalata da dalibansu domin ba su maki mai lakabin S*x-for-grades a ranar Litinin, uwar gidan gwamnan jihar Ekiti, Erelu Bisi Fayemi ta bayyana cewa itama wasu sun nemi yin lalata da ita a lokacin da ta ke jami'a.

Hakan na zuwa ne bayan fitowar faifan bidiyon na BBC Afirca Eye da ke nuna wani bangare na binciken da wasu 'yan jarida suka gudanar yayin da suka badda kama a matsayin dalibai a jami'oin Legas a Najeriya da Jami'ar Ghana da ke Legon.

DUBA WANNAN: An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

An fara nuna wa wasu 'yan tsirarun mutane bidiyon binciken a Legas ciki har da wakiliyar First Lady, Aisha Buhari da matar Gwamna Fayemi da wasu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A yayin da ta ke karin bayani, Uwargidan Fayemi ta ce tayi sa'a abin bai yi nisa ba amma "ko kadan babu dadi."

Ta kallubalanci mata su daure su fito su tona asirin wadanda suke neman cin zarafin su domin "an dade ana shiru kan lamarin."

A cewar ta, a matsayin ta na shugaban kungiyar matan gwamnoni, kungiyar za ta dauki mataki a dukkan jihohin Najeriya 36 domin kawo karshen wannan mummunan annoban.

Ta ce rashin naukan abin da muhimmanci ne ya janyo har yanzu ba a kawo karashen lamarin ba inda ta kara da cewa abin ya shafi kowa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel