Ku harbi duk wanda ya yi yunkurin tare tawaga ta - Zababben gwamnan PDP

Ku harbi duk wanda ya yi yunkurin tare tawaga ta - Zababben gwamnan PDP

- Dave Umahi, Gwamnan jihar Ebonyi, ya bawa jami'an tsaronsa umarnin su harbe duk wanda ya yi yunkurin tare tawagarsa yayin da take tafiya

- Gwamnan ya bayar da wanna umarnin ne yayin da yake bayar da labarin yadda wasu masu zaman makoki suka tare masa hanya da gangan domin su ci masa mutunci

- Umahi, zababben gwamna a jam'iyyar PDP, ya yi ikirarin cewa wadanda suka tare masa hanya sun harba bindiga

Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya bawa jami'an tsaronsa umarni harbe duk wanda ya yi yunkurin tare tawagarsa yayin da take tafiya.

Jaridar PremiumTimes ta rawaito cewa gwamnan ya bayar da wanna umarnin ne yayin da yake bayar da labarin yadda wasu masu zaman makoki suka tare masa hanya da gangan domin cin mutuncinsa a cikin jihar.

Lamarin ya faru ne a kan titin Onicha a karamar hukumar Onicha da ke yankin jihar Ebonyi yayin da gwamnan ke kan hanyarsa ta komawa Abakaliki daga mahaifarsa, Uburu, da yammacin ranar Juma'a.

Gwamnan ya yi ikirarin cewa wadanda suka tare masa hanya sun harba bindiga.

"An tare min hanya a Onicha a daren ranar Juma yayin da na tsaya domin duba wani aiki a hanya ta dawowa Abakaliki daga Uburu da misalin karfe 12:00 na dare.

"Duk da yawan jami'an tsaro na sojoji da 'yan sanda dake tare da ni basu bude min hanya ba. Nan take na ce a kama su gaba daya, amma sai mafi yawansu suka gudu. Ina tunanin ma sun dauke bindigar daya daga cikin sojojin da ke tawaga ta," a cewar gwamna Umahi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel