Kayayyakin da gwamnati ba ta sanya wa haraji ba a Najeriya

Kayayyakin da gwamnati ba ta sanya wa haraji ba a Najeriya

A ranar Talata, 8 ga watan Oktoban da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gabatar da daftarin kasafin kudin kasa na badi na naira tiriliyan 10.7 a zauren majalisun dokoki na tarayya.

Kamar yadda jaridar BBC Hausa ta ambato shugaban kasar yana cewa, gwamnatin sa ta gina kasafin kudin kasar ne a kan kudin harajin kayayyaki wanda a harshen turanci ake kira VAT (Value Added Tax).

A zakule-zakulen da jaridar Legit.ng tayi, an samu sauye-sauye da dama a kasafin kudi da aka ware wa wasu ma'aikatun kasar idan an kwatanta da na bana wanda shugaban kasar ya gabatar tun a bara.

Ana iya tuna cewa, a baya-bayan nan ne majalisar tattalin arziki tare da shugaban kasar suka kara yawan haraji daga kaso 5 cikin 100 zuwa kaso 7.5 cikin 100.

KARANTA KUMA: Buhari ya yi alhinin rayukan da suka salwanta sanadiyar kiferwar jirgin ruwa a Bauchi

Kamar yadda shugaban kasar ya zayyana, dokar harajin ta ba ta da hadi da magunguna, kayan koyo da karantarwa da kayan more rayuwa.

Ya ce sashe na 46 da dokar kudi ta 2019 ta fadada, akwai kayayyakin da karin harajin na VAT ba zai shafe su ba da suka hadar da:

Biredi fari ko ruwan kasa

Masara da shinkafa da alkama da gero da dawa

Kifi da danginsa

Fulawa da sauran dangin abinci masu alaka da ita.

Kayan itatuwa wato kayan marmari da abubuwa masu kwanso da ganyaye

Doya da gwaza da dankalin gida da na turawa

Nama da 'kwai

Madara

Gishiri da sunadaran dandano da kayan kamshi

Ruwa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel