Buhari ya yi alhinin rayukan da suka salwanta sanadiyar kiferwar jirgin ruwa a Bauchi

Buhari ya yi alhinin rayukan da suka salwanta sanadiyar kiferwar jirgin ruwa a Bauchi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa tare da alhinin wata mutuwar yawa da ta auku sanadiyar kifewar jirgin ruwa wadda ya dulmiye da kimanin mutane 38 a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya.

Cikin sakon ta'aziyya tare da bayyana alhini da ya gabatar a ranar Talata cikin birnin Abuja da sanadin mai magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, shugaban kasa Buhari ya bayyana damuwa matuka wanda ya ce ba ta takaita kadai a kan 'yan uwan wadanda suka yi rashin ba domin kuwa ya shafi kasar nan baki daya.

Buhari ya kuma jajintawa gwamnati da daukacin al'umma jihar Bauchi, inda ya nemi da a dage wajen kwarara addu'o'in rokon jinkai da rahama ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, kimanin rayukan mutane 38 ne suka salwanta a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku cikin kauyen Kuna da ke karamar hukumar Kirfi ta jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

KARANTA KUMA: INEC za ta dauki ma'aikata 16,139 na wucin gadi kan zaben gwamnan jihar Kogi

Legit.ng ta ruwaito cewa, lamarin ya auku ne da tsakar ranar Litinin da ta gabata yayin da jirgin ya dauko dakon manoma da 'yan kasuwa da ke kauyen da abin ya faru.

A wani rahoto mai nasaba da wannan muka kalato daga jaridar BBC Hausa mun samu cewa, wata amarya da 'yan uwanta uku sun nutse a wata madatsar ruwa yayin da suke yunkurin daukar hoton irin na zamani wato 'selfie' kamar yadda 'yan sanda a jihar Tamil Nadu da ke kudancin Indiya suka bayyana.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel