Ma'aikatun gwamnatin tarayya da suka samu kaso mafi tsoka a kasafin kudin 2020

Ma'aikatun gwamnatin tarayya da suka samu kaso mafi tsoka a kasafin kudin 2020

A ranar Talata, 8 ga watan Oktoban 2019 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gabatar da daftarin kasafin kudin Najeriya na badi a zauren 'yan majalisar tarayya da ke babban birnin kasar nan wato Abuja.

Shugaban kasar ya gabatar da daftarin kasafin kudin kasa wanda ake sa ran za'a a kashe a badi da ya haura naira tiriliyan 10 tamkar yadda ya kasance a shekarar da muke ciki.

Rahoton da jaridar Vanguard ta ruwaito ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasa na badi wanda ya tasar ma naira tiriliyan 10.726.

A zakule-zakulen da jaridar Legit.ng tayi, an samu sauye-sauye da dama a kasafin kudi da aka ware wa wasu ma'aikatun kasar idan an kwatanta da na bana wanda shugaban kasar ya gabatar tun a bara.

KARANTA KUMA: INEC za ta dauki ma'aikata 16,139 na wucin gadi kan zaben gwamnan jihar Kogi

A yayin da aka ware kusan tiriliyan biyu da rabi na kudin da za a batar a 2020 wajen biyan bashin da ke kan kasar, ga dai yadda dalla-dalla aka yi wa ma'aikatun kasar tanadi:

Ayyuka da gidaje - N262bn

Sufuri - N123bn

Hukumar ilimin matakin farko; UBEC - N112bn

Majalisar dokoki - N125bn

Ma'aikatar Shari'a - N110bn

Tsaro - N100bn

Noma - N83bn

Ruwa - N82bn

Neja-Delta - N81bn

Masana'antu da zuba jari - N40bn

Ilimi - N48bn

Lafiya - N46bn

Hukumar raya Arewa maso Gabas; NEDC - N38bn

Shirye-shiryen tallafi (Social Investment Programmes) - N30bn

Birnin Tarayya Abuja - N28bn

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel