Kada kowace ma'aikatar gwamnatin tarayya ta sake daukar aiki ba tare da na lamunce ba - Buhari

Kada kowace ma'aikatar gwamnatin tarayya ta sake daukar aiki ba tare da na lamunce ba - Buhari

A yayin gabatar da kasafin kudin kasa na 2020 a ranar Talata, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gindaya sharadin daukar aiki ga dukkanin ma'aikatu da cibiyoyin gwamnatin tarayya na kasar.

Shugaba Buhari kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, ya gargadi dukkanin ma'aikatu da cibiyoyin gwamnatin tarayya da su nemi lamuninsa gabanin yanke shawarar daukar ma'aikata aiki.

Shugaban kasar ya ce daga karshen watan Oktoba zuwa farkon watan gobe na Nuwamba, kada ma'aikatar gwamnatin tarayya da ta sake yunkurin daukar ma'aikata aiki face ta nemi izininsa ko kuma ta fuskanci hukunci.

Haka kuma shugaban kasa Buhari cikin jawabansa na gabatar da daftarin kasafin kudin 2020, ya yabawa majalisar dokoki ta tarayya kasar dangane da kokarin hadin kai na aiki tare da majalisar zartarwa.

KARANTA KUMA: Dangote da Sarkin Kano sun shawarci gwamnati a kan bunkasa tattalin arzikin Najeriya

A rahoton da BBC Hausa ta ruwaito, shugaba Buhari ya ce daftarin kasafin kudin zai kara harajin kayayyaki daga kaso 5 cikin 100 zuwa 7.5 cikin 100.

Ya ce za a yi amfani da harajin ne wurin inganta fannin kiwon lafiya da ilimi da gine-ginen hanyoyi inda ya bukaci majalisar tarayyar da ta guji yin tsaiko wajen amince wa da kasafin kudi, al'amarin da ya janyo tsaiko a kasafin kudin shekarun da suka gabata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel