Dangote da Sarkin Kano sun shawarci gwamnati a kan bunkasa tattalin arzikin Najeriya

Dangote da Sarkin Kano sun shawarci gwamnati a kan bunkasa tattalin arzikin Najeriya

A kasar Najeriya wasu fitattun masana tattalin arziki, manyan ma'aikatan banki da 'yan kasuwa, a jiya Litinin sun yi kyakkyawan yunkuri na bai wa gwamnatin kasar nan sahihan shawarwari kan yadda za ta bunkasa tattalin arzikin kasar.

Masana tattalin arzikin sun zayyana hangen nesa duba da kwarewa a yayin babban taron tattalin arzikin Najeriya karo na 25 da ya gudana cikin babban birnin kasar na tarayya wato Abuja.

Wadanda suka baje kwarewarsu wajen bayar da shawarwari a yayin taron sun hadar da fitaccen attijirin nahiyyar Afirka, Aliko Dangote, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma sarkin jihar Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi na II, shugabar bankin farko na Najeriya, Mrs Ibukun Awosika, shugaban Majalisar tattalin arziki (EAC), Dr. Doyin Salami da kuma gogaggen ma'aikacin banki, Atedo Peterside.

Dukkanin su sun bayar da shawarwari dangane da yadda gwamnatin Najeriya za ta magance kalubalen da tattalin arzikin kasar ke fuskanta gami da dasa hanyoyin fidda mafiya akasarin al'ummar kasar daga kangi na talauci.

Yayin babban taron Dangote ya ce dole ne gwamnatin ta inganta masana'antun kasar matukar ta nufaci kawo gyara na bunkasar tattalin arziki, lamarin da ya ce masana’antun Najeriya na tallafawa ne da kashi 9 kacal cikin dari maimakon akalla kashi 30 da ya kamata ace bangaren na bunkasa tattalin arzikin kasar.

Haka kuma gawurtaccen attajirin ya ce matukar za a bunkasa bangaren masana’antu a kuma gyara hanyoyin sufuri musamman bangaren jiragen kasa baya ga fadada tashoshin ruwan kasar don saukaka hanyar fita da kuma shigo da halastattun kayayyaki, babu shakka zai taimaka matuka wajen fidda tattalin arzikin kasar zuwa tudun tsira.

KARANTA KUMA: A gaggauta daukar mataki kan keta haddin dalibai da malamai ke yi a jami'o'i - Aisha Buhari

Bugu da kari Dangote wanda an yi itifakin cewa ya fi dukkanin wata bakar fata arziki a doron kasa, ya shawarci gwamnati da ta kara kaimi wajen magance matsalar fasakwauro wadda ke yiwa tattalin arzikin Najeriyar zagon kasa tare kuma da bunkasa harkokin samar iskar gas da kuma bangaren musayar kudade.

A nasa bangaren Mai martaba sarkin Kano wanda babu shakka muke fatan Mai Duka ya ci gaba jan zamaninsa, ya bayyana damuwa kwarai da aniya dangane da kawo wa yanzu gwamnati ta gaza shimfida managartan tsare-tsare masu tasiri wajen tabbatar da ci gaba a kasar duba da yawan al’ummar da Najeriya ta kunsa.

Sarki Sunusi ya ce yawan jama'a a Najeriya na da babbar nasaba da kalubalen da kasar ta ke fuskanta kama daga ta'adar masu garkuwa da mutane, fashi da makami, ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram da kuma ta'ammali da miyagun kwayoyi wanda dukkaninsu sun janyo durkushewar tattalin arziki.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel