Tsohuwar matar dan Atiku ta zarge shi da sace 'yaya uku da suka haifa tare

Tsohuwar matar dan Atiku ta zarge shi da sace 'yaya uku da suka haifa tare

A wani labari da ta wallafa, Maryam Sheriff, tsohuwar matar dan Atiku Abubakar ta bayar da labarin yadda tsohon mijinta ya sace 'ya'ya uku da suka haifa tare sannan kuma ya yi mata korar wulakanci daga gidansa.

A cewar ta, "sunana Maryam Sheriff, tsohuwar matar dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubkarar. Mun rabu nu da mijina bisa tsarin shari'ar Musulunci, saboda yawan samun sabanin da muke yi.

"Bayan rabuwar mu babu dade wa sai 'ya'yan mu da muka haifa tare su uku suka fara nuna bukatar suna son ganin mahaifinsu. Da naga lokacin zagayowar ranar haihuwan daya daga cikinsu ta zagayo sai na yi masa maganar cewa yara na yawan tamabayar shi. Hakan tasa ya zo gidanmu a ranar 10 ga watan Maris.

"Lokacin da ya zo gidan mu har yaran sun yi shirin barci, amma sai yace yana son fita da su domin yi musu sayayya tare da saya wa mai murnar zagayowar ranar haihuwa kyatuttuka. Nan da nan na shirya yara. Har zasu fita sai na yi zargin cewa ba lallai ya dawo da su ba, a saboda haka sai na nuna masa rashin amincewa ta da fitarsu.

"Da ya ga haka sai ya ce zan iya shirya wa mu fita tare idan ban yarda da shi ba, har na shiga cikin motar za mu fita tare sai na ji kai na ya fara yi min ciwo, sai na fita daga motar, na ce su tafi kawai.

"Da naga dare ya fara yi amma basu dawo ba sai na fara kiran lambar wayarsa, amma ba ya amsa wa. Nan da nan na fita zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusa na shaida musu cewa miji na ya zo ya dauke min yara. Nan take suka karbi lambarsa suka kira shi, amma da suka fada masa dalilin kiran sai ya kashe wayarsa, kuma ya ki daga kiran da aka kara yi masa

"Na koma gida na cigaba da kiransa, lamarin da yasa daga baya ya amsa tare da fada min cewa har duniya ta nade ba zan kara sa yaran a idona ba."

Maryam ta ce haka tsohon mijin nata ya tafi da yaranta guda biyar; uku da suka haifa tare da kuma diyar da ta haifa da tsohon mijinta da kuma wata yarinya da take riko.

Ta kara da cewa amma daga baya ya dawo da diyarta da ta haifa tare da tsohon mijinta bayan ta matsa wa jami'an 'yan sanda lamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel