'Shisha' na dauke da sinadaran cutar daji (kansa) - Sabon bincike daga kasar Dubai ya nuna

'Shisha' na dauke da sinadaran cutar daji (kansa) - Sabon bincike daga kasar Dubai ya nuna

Sinadaran karfe da kan janyo cutar daji da aka fi sani da kansa na kunshe da yawan gaske cikin kayan shakatawa na 'Shisha' da Medwakh fiye da sigari, sabon binciken kasar UAE ya bayyana.

Malaman kimiyya a Sharjah da Abu Dhabi sun samu cewa idan aka hada hadarin Shisha da Sigari, sinadaran nickel, chromium, copper da zinc masu cutarwa sun fi yawa cikin Shisha.

Wannan bincike ya biyo bayan wani binciken da aka wallafa a farkon shekarar nan da ya nuna cewa kwayoyin cuta cikin Shisha fiye da sigari.

Malaman Kimiyyan sun kara da cewa masu shan Shisha na yiwa kansu barazanar kamuwa da cutar dajin huhu.

Malamar Kimiya a jami'ar Sharjah, Ayesha Mohammed, ta bayyana cewa: "Tiyon Shisha da Medwakh basu da matata, saboda hakan sinadarai masu cutarwa kan iya shiga cikin huhu kuma su haddasa cututtuka irinsu cutar dajin huhu da baki, cutar zuciya."

"Ba zan taba baiwa wani shawaran shan Shisha da dokha ba. Shan shisha kamar loda bindiga da harsasai ne, lokaci zai harba shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel