Mai garkuwa da mutane ya sace jariri yayin da mahaifiyarsa ke bacci

Mai garkuwa da mutane ya sace jariri yayin da mahaifiyarsa ke bacci

Jami'an rundunar 'yan sanda a jihar Ogun sun kama wani mutum Olakunle Agbaje, mai shekaru 39, bisa zarginsa da sace wani jariri mai watanni biyu yayin da mahaifiyarsa ke barci.

Ana zargin Agbaje da lallaba wa gidan matar, Marufu Taiwo, dake unguwar Mowe a karamar hukumar Obafemi-Owode, jihar Ogun tare da sace mata jaririnta yayin da take barci.

A cikin jawabin da ya fitar ranar Litinin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai.

Oyeyemi ya ce sun kama mai laifin ne ranar Asabar bayan sun samu kirann gagga wa daga ofishin 'yan sanda na yankin Mowe.

DUBA WANNAN: A karo na farko: Sanata Marafa ya ziyarci gwamna Matawalle, ya yi magana a kan zamansa a APC

"Mahaifiyar jaririn ta tashi a daidai lokacin da mai laifin ke kokarin fita daga dakinta a rungume da jaririn.

"A yayin da yake amsa tambayoyi, mai laifin ya ce ya yi nadamar abinda ya aikata tare da bayyana cewa bai san abinda ya kai shi ga aikata hakan ba," a cewar Oyeyemi.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Bashir Makama, ya bayar da umarnin a mayar da mai laifin sashen binciken manyan laifuka domin zurfafa bincike da gurfanar da shi a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel