Jihohi 31 na fama da talauci matuka a kasar – Inji Buhari

Jihohi 31 na fama da talauci matuka a kasar – Inji Buhari

Rahotanni sun kawo ceewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci attajiran ‘yan Najeriya da su duba yiwuwar bunkasa tattalin arzikin kasar ta hanyar mai da hankali wajen kirkiro sana’o’i, bunkasa harkokin kasuwanci, cinikayya da gina kasa kasar ta hanyar amfani da albarkatun da Allah yayi wa kasar.

Buhari ya yi wannan kira ne a taron habbaka tattalin arzikin kasar karo ta 25 wanda aka gudanar a Abuja, a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba.

Shugaban kasar ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki da kamfanoni masu zaman kansu domin habbaka tattalin arzikin kasar da kuma tsara manufofi na ci gaba a Najeriya.

“An sanar da ni cewa taron na wannan shekara zai maida hankali ne wajen tsara hanyoyin da zasu samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya a musamman harkokin Noma, Hako Ma’adinai, Fasaha da Kere-Kere, da kuma kuma ayyukan Komfuta.

“A tattaunawar da muhawarar da kwararru za su yi a wannan taro, ina son in yi kira gareku da ku maida hankali wajen tsara hanyoyin da za a samu nasara ne a harkokin samun ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kasa ta yadda Najeriya zata amfana da su.”

Shugaban kasar ya kara da cewa: “Najeriya kasa ce da ke da al’umma kusan miliyan 200 a cikin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja. Mafi yawan arzikin kasar ya na dankare ne a wasu jihohin da basu wuce hudu ko biyar ba tare da babban birnin tarayya. Wasu daga cikin attajiran kasar nan na zaune a cikin wannan dakin kuma sun sani.

KU KARANTA KUMA: Sulhu da yan ta’adda ba zai taba magance matsalolin tsaro ba – Tsohon Janar din soja

“A haka kenan jihohi 31 dake da mutane akalla miliyan 150 na zaman hannu baka hannu akushe ne da ya sa a yanzu kasa ke ta fama da matsalolin tsaro da yaki ci yaki cinyewa. Hakan yasa kasashen da ke kewaye da Najeriya na fama da irin wadannan matsaloli."

Bayan nan ya yaba da yadda aka gudanar da zabukan 2019, da kuma yadda wadanda basu yi nasara ba suka nufi kotu domin kai kukan su. Buhari yace hakan ya nune cewa lallai an samu ci gaba matuka ta fuskacin siyasa da dimokradiyya a kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel