MURIC ta yi Allah wadai korar daliba daga makaranta saboda ta sanya Hijabi

MURIC ta yi Allah wadai korar daliba daga makaranta saboda ta sanya Hijabi

Kungiyar kare hakkin Musulmai a Najeriya MURIC, ta bayyana rashin jin dadinta kan korar daliba daga makarantar sakadandaren jami'ar Ibadan, Ikhlas Badiru, daga makaranta.

Shugabar makarantar da kanta mai suna, Phebean Olowe, ta sallami dalibar.

Diraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, a wani jawabi da ya saki ranar Litinin ya nuna bacin ransa kan wannan abu.

Yace: "Ya bayyana karara cewa shugabar makarantar bata iya sulhu ba kuma bata ki abubuwa su tabarbare ba."

"A Turai da Amurka inda Musulmai ba su yawa, an halatta sanya hijabi a makarantu."

KU KARANTA: Cikin shirin gabatar da kasafin kudin 2020 gobe, Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC na musamman

Mun kawo muku rahoton cewa a ranar 26 ga Satumba, hukumar makarantar ta dakatar dalibar makarantar Ikhlass Olasubomi Badiru, saboda ta sanya hijabi ta je makarantar da shi a watan Yulin da ya gabata.

Idan ba a manta ba watannin da suka gabata iyayen daliban makarantar sun nemi makarantar ta hana dalibai mata sanya hijabi idan za su shiga makarantar.

A wata wasika da shugaban makarantar mai suna Phebean Olowe ya rubuta a ranar Litinin dinnan da ta gabata, shugaban makarantar ya bayyanawa dalibar cewa makarantar ta dakatar da ita na tsawon mako biyu, kuma za ta tsaya da zuwa makarantar daga ranar 7 ga watan Oktoba zuwa ranar 18 ga watan Oktoba, 2019.

Makarantar dai ta yankewa dalibar hukunci ne bayan kan cewa makarantar an kama da laifin karya dokar makaranta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel