Sulhu da yan ta’adda ba zai taba magance matsalolin tsaro ba – Tsohon Janar din soja

Sulhu da yan ta’adda ba zai taba magance matsalolin tsaro ba – Tsohon Janar din soja

Wani tsohon soja, Manjo Janar Cecil Esekhaigbe ya bayyana cewa shiga yarjejeniyar sulhu da yan ta'adda ba zai magance matsalolin da kasar ke fuskanta ta bangaren tsaro ba.

Esekhaigbe ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, a lokacin da yake jawabi a shirin Channels Television na Sunrise Daily, kusan sa’o’i 48 bayan yan bindiga sun saki mutane 15 a jihar Katsina, sakamakon yarjejeniyar da suka shiga da gwamnan jihar, Aminu Masari.

Yayin da yake cigaba da jawabi, Esekhaigbe yayi kira ga samun cikakken hadin kai tsakanin hukumomin tsaro a kasar.

Tsohon jami’in sojan ya yada cewa idan aka yada bayanan kwararru aka kuma yi amfani da su yanda ya kamata, tabbas za a kawo karshen ta'addanci wadanda suka hada da sace-sacen mutane, fashi da makami, da sauran su.

Yayin da yake magana akan ingantaccen tsaron kasar, yayi kira da a tura kudi yanda ya kamata tare da horar da rundunar yan sandan Najeriya.

Gwamna Aminu Masari a watan Agusta ya shiga yarjejeniya tare da yan bindiga a mafakarsu, don tabbatar da zaman lafiya a jihar.

KU KARANTA KUMA: APC a Katsina na yunkurin hukunta Ministan Buhari da dan uwansa

A cewar hadimin Masari, Mista Abdu Labaran, an yanke shawaran ne a wani gagarumin taro wanda ya shafi tsaro.

Yarjejeniyar yayi sanadiyar sakin mutane 30 da yan bindigan suka sace a watan Satumba bayan yanta mutane 15 a lamari makamancin haka.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel