PDP tayi nasara yayinda kotun zabe tayi watsi da karar APC, ta tabbatar da nasarar gwamnan Bauchi

PDP tayi nasara yayinda kotun zabe tayi watsi da karar APC, ta tabbatar da nasarar gwamnan Bauchi

Kotun da ke sauraron karar zaben gwamna a jihar Bauchi, ta jaddada nasarar zaben Gwamna Bala Mohammed na jam'iyya Peoples Democatic Party (PDP).

Yayin da yake gabatar da hukunci na tsawon awa shida a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, shugaban kwamitin mutane uku na kotun, Justis Salihu Shuibu, ya sanar da sokewar karar da jam’iyyar All Progressive Congress (APC) da dan takaranta, Mohammed Abubakar suka shigar.

Justis Salihu Shuibu ya yanke hukuncin cewa karar da APC da dan takaranta Barista Mohammed Abubakar suka shigar akan jam’iyyar PDP da dan takaranta, Sanata Bala Mohammed bai da inganci.

A baya kotun ta yi watsi da jawabai kan rantsuwan 27 daga cikin 33 da shaidun da All Progressives Congress ( APC) da dan takaranta Mohammed Abubakar suka gabatar.

Mai shari’an ya bayyana cewa masu karan sun gaza tabbatar da ingancin karar su.

KU KARANTA KUMA: APC a Katsina na yunkurin hukunta Ministan Buhari da dan uwansa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa an karfafa tsaro a ciki da wajen kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Bauchi yayinda Alkalan kotun ke zaman raba gardama tsakanin gwamnan jihar, Bala Mohammad na jam'iyyar PDP da Mohammed Abubakar na jam'iyyar APC.

Jami'an tsaro wadansa suka hada da yan sanda, jami'an NSCDC, jami'an DSS da wasu na leken asiri sun mamaye titin Ahmadu Bello way da titin Yandoka da safiyar nan.

Punch ta ruwaito cewa an kulle hanyar gaba daya kuma an umurci mutane su bi wasu hanyoyin daban.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel