Yawan jama'ar Najeriya ya zamar wa gwamnati alakakai - Sarki Sanusi II

Yawan jama'ar Najeriya ya zamar wa gwamnati alakakai - Sarki Sanusi II

Sarkin Kano, mai marta Muhammadu Sanusi II, ya ce hauhawar yawan 'yan Najeriya ya zamar wa kasa alakakai.

Sarki Sanusi II ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wurin wani taro a kan tattalin arziki da ke gudana a Abuja.

Taron ya samu halartar shugaban cibiyar 'Kukah Centre', Bishop Mathew Hassan Kukah, da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.

An shirya taron ne domin tattauna wa a kan yadda za samar damarmakin yin kasuwanci ga 'yan kasa da kuma kalubalen da yawam jama'a ke da shi ga tsaro da zaman lafiya mai dore wa.

DUBA WANNAN: Tsirarun mutane da ke zaune a jihohi 5 sun tattare arzikin Najeriya - Buhari

Basaraken ya ce har yanzu babu tsare-tsare a kasa da zasu tabbatar da cewa an yi amfani da yawan jama'ar da ake da shi domin samun cigaba a kasa.

Sarki Sanusi ya alakanta yawaitar matsalar garkuwa da mutane, fashi da makami, da rikicin manoma da makiyaya a kan hauhawar yawan jama'a.

"Mutane na yawan cewa yawan mu tamkar wata haja ce, amma ba haka bane, saboda ba mu kai ga wannan gwadaben ba har yanzu. Yawanmu a hakin yanzu ya zama alakakai, saboda dukkan matsalolin da muke fuskanta na garkuwa da mutane, fashi da makami, Boko Haram, tu'ammali da miyagun kwayoyi nada alaka da hauhawar yawanmu. har yanzu babbar tambayar ita ce; ta yaya za mu amfana daga yawan jama'ar da muke da shi?," a cewar sarki Sanusi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel