Yahaya Bello ya zauna da James Faleke a game da zaben jihar Kogi

Yahaya Bello ya zauna da James Faleke a game da zaben jihar Kogi

Mun samu labari cewa a yunkurin jam’iyyar APC mai mulki na ganin ta cigaba da rike jihar Kogi, an yi wani zama tsakanin gwamna mai-ci Alhaji Yahaya Bello da wani babban Jigon APC.

Mai girma Yahaya Bello ya karbi bakuncin Honarabul James Abiodun Faleke ne a gidansa na babban birnin tarayya Abuja. An yi wannan ganawa ne a Ranar Lahadi, 6 ga Oktoban 2019.

Kamar yadda babban Sakataren yada labarai na gidan gwamnatin jihar Kogi, Onogwu Muhammed, ya bayyana, an yi wannan ganawa ne domin karawa jam’iyyar APC karfi a jihar.

Mista Muhammed yake cewa wannan ya na cikin shirin da APC ta ke yi na ganin ta samu nasara a zaben gwamnan da za a yi a cikin tsakiyar Watan Nuwamban da za a shiga a shekarar nan.

KU KARANTA: Ana cigaba da shirya yadda za a yaki Osinbajo a zaben 2023

Bello da kuma 'dan majalisar wakilan na Legas watau James Faleke sun tattauna ne domin ganin yadda za su bullowa zaben gwamnan da za ayi kamar yadda Onogwu Muhammed ya bayyana.

Jagororin na APC a jihar Kogi sun dauki hotuna cikin farin ciki bayan wannan muhimmin taro da aka yi. ‘Dan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC, Edward Onoja ya halarci zaman.

Onoja wanda ke rike da mukamin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Kogi shi ne Abokin takarar Yahaya Bello a zaben na bana bayan gwamnan ya samu matsala da mataimakinsa.

James Faleke ya fito nemi kujerar gwamna a 2015 a matsayin Abokin takarar Marigayi Abubakar Audu wanda ya rasu ana tsakiyar zabe bayan sun doke Yahaya Bello wajen neman tikitin APC.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel