Dan takarar gwamna a PDP ya yaba ma Buhari, yace shugaban kasar na nufin Najeriya da alkhairi

Dan takarar gwamna a PDP ya yaba ma Buhari, yace shugaban kasar na nufin Najeriya da alkhairi

Dan takaran gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ogun a zaben 2019 na kasa, Sanata Buruji Kashamu yace shugaban kasa Muhammadu Buhari na nufin Najeriya da alkhairi idan aka yi la’akari da manufofin gwamnatinsa wajen gyaro rashin isasshen kayayyakin more rayuwa a kasar.

A wata hira da manema labaai a karshen makon da ya gabata, Kashamu ya bukaci yan Najeriya da su marawa Shugaban kasar baya saboda wannan manufa nasa.

Kashamu yace ya kuma yi farin ciki da kokarin gwamnatin Buhari wajen kawo cigaba ga talakawan Najeriya ta hanyar yanta kananan hukumomi daga gwamnoni domin suma su ci gashin kansu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya na gab da kwace kadarorin Maina na miliyoyin naira a Najeriya da kasar waje

Dan siyasan wanda ya bayyana cewa bai bar jam'iyyar PDP ba, yace yaki da rashawa ya cancanci samun goyon bayan dukkanin yan kasar, muddin Najeriya na son ta rayu, inda yace "ya zama dole a cire siyasa da kabilanci a lamarin."

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa wani matashi dan asalin garin Ribah dake karamar hukumar Danko Wasugu a jihar Kebbi ya hau falwayan karfen kamfanin sadarwan Glo dake garin Ribah da cewar bai zai sauka ba, sai shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi murabus daga kujerasa

A lokacin, Shugaban jam'iyya na Danko Wasagu yace zai baiwa matsahin kyautar sabon babur idan har ya sauko amma ya kiya. Amma daga baya, an samu daman shawo kansa inda ya sauko kuma aka tafi da shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel