Cikin shirin gabatar da kasafin kudin 2020 gobe, Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC na musamman

Cikin shirin gabatar da kasafin kudin 2020 gobe, Shugaba Buhari ya jagoranci taron FEC na musamman

Yayinda zai gabatar da kasafin kudin kasa ta shekarar 2020 a gobe Talata gaban majalisar dokokin tarayya, Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zantarwa na musamman a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, 2019.

A al'ada, ranar Laraba ake zaman majalisar amma saboda kasafin kudin da zai gabatar, ministoci sun hallara domin dubi na karshe cikin kasafin kudin kafin gabatar da shi gaban yan majalisa.

Wannan shine kasafi kudi na farko da shugaban kasa zai gabatar ga majalisar karkashin jagorancin Sanata Ahmad Lawan da kakaki Femi Gbajabiamila.

Lokacin da ya gabatar da kasafin kudi na karshe ga tsohon shugaban majalisa Bukola Saraki, abun bai yi kyau yayinda yan majalisan suka rika yi masa ihu bamaso.

Abin mamakin shine, cikin dukkan wadanda suka yi masa ihu a shekarar 2018 mutum daya ne kacal ya samu dawowa majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel