Gwamnatin tarayya na gab da kwace kadarorin Maina na miliyoyin naira a Najeriya da kasar waje

Gwamnatin tarayya na gab da kwace kadarorin Maina na miliyoyin naira a Najeriya da kasar waje

Hukumar yaki da cin hanci da ashawa (EFCC) ta cika takardun kotu domin kwace wasu adadin kadarori da aka gano suna da nasaba da tsohon Shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina.

Hakazalika, hukuma yaki da rashawar ta cika wani takarda domin samun umurnin tsare tsohon mataimakin daraktan na hukumar ta CIPPO, wanda a makon da ya gabata ne hukumar tsaro na sirri DSS suka mika shi ga EFCC bayan sun kama shi a wani otel a Abuja.

Wata babbar majiya ta bayyana cewa EFCC ta gano gidaje da dama daruruwan miliyoyi a gida da waje wadanda ke da nasaba da Maina.

Baya ga gidaje EFCC ta gano kamfanoni biyar wadanda tayi ikirarin cewa Maina na amfani dasu wajen hamdame kudi sannan kuma ta bukaci ya samar da cikakken bayanin kudi dake asusun kamfanonin.

Jerin kamfanonin sune; Cluster Logistics, Drew Investment & Construction Ltd, Kongolo Dynamics Cleaning Ltd, “Dr” AbduUahi A. Faizal, Nafisatu Aliyu Yeldu and Abdulrasheed Abdullahi Maina.

KU KARANTA KUMA: An tsige mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Taraba

Akwai alamu dake nuna cewa za a gurfanar da Maina a gaban kotu a wannan makon domin amsa tuhume-tuhumen hukumar yaki da rashawa da Gwamnatin tarayya a kansa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel