Sanata Marafa da jigajigan 'yan APC sun ziyarci gwamna Matawalle a gidan gwamnatin Zamfara

Sanata Marafa da jigajigan 'yan APC sun ziyarci gwamna Matawalle a gidan gwamnatin Zamfara

A karo na farko, Jagoran tsagin jam'iyyar APC a jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya gana da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, tare da bayyana cewa har yanzu shi dan jam'iyyar APC ne.

Korafin da Marafa, sanatan APC a wancan lokacin, ya gabatar a gaban kotu ne ya jawo aka kwace dukkan kujerun APC a jihar Zamfara tare da mika su ga 'yan takarar jam'iyyar PDP.

Tsohon Sanatan ya shaida wa gwamna Matalle cewa ya ziyarce shi ne tare da sauran jiga-jigan 'ya'yan jam'iyyar APC masu biyayya ga tsaginsa domin tabbatar masa da goyon bayansu, musamman a wannan lokaci da ake bukatar zaman lafiya a jihar Zamfara.

A wani jawabi da aka fitar a Abuja, Marafa ya bayyana cewa; "wannan ba lokacine na siyasa ba. Allah kan iya bayar da mulki ga duk wanda ya so, kuma a lokacin da yaso. Mun ga hakan a jihar Zamfara. Kasancewar Matawalle gwamna darasi ne daga Allah, a saboda haka bama jayayya da yin Allah.

"A lokacin gwamnatin baya wasu mutane sun dauka cewa muna siyasa ne kawai, amma yau ga shi cikin yardar Allah mun samu zaman lafiya a jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: Wata dattijuwa mai shekaru 87 ta mutu ta bar jikoki 102 a Zamfara

"Hatta shugaba Buhari, wanda shine shugaba mafi daraja a jam'iyyar APC, ya yaba wa gwamna Matawalle a kan dawo da zaman lafiya a jihar Zamfara, hakan shine abinda muke bukata tuntuni," a cewar Marafa.

Da yake magana a kan kasancewarsa mamba a jam'iyyar APC, Marafa ya bayyana cewa; "ina son yin amfani da wannan dama domin tabbatar wa da mutanen jihar Zamfara da Najeriya cewa har yanzu ni mamba ne a jam'iyyar APC kuma jam'iyyar APC a jihar Zamfara guda daya ce kuma Alhaji Sirajo Maikatako ne shugabanta."

A jawabinsa, gwamna Matawalle ya gode wa Marafa da mabiyansa a kan goyon baya da addu'ar da suke yi masa da kuma fata nagari da suke yi wa jihar Zamfara da jama'arta.

Kazalika, gwamna Matawalle ya ce wasu makiya jihar Zamfara sun yi yunkurin tayar da hankalin jama'ar jihar yayin da ya yi bulaguro zuwa kasar waje, tare da bayyana cewa babu abinda zai dauke hankalin gwamnatinsa daga kudirinta na ganin cewa an samu zaman lafiya mai dore wa a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel