Hassada ake yi da tauraruwar Yemi Osinbajo – Inji Fasto Adeboye

Hassada ake yi da tauraruwar Yemi Osinbajo – Inji Fasto Adeboye

Babban Limamin cocin nan na RCCG, Fasto Enoch Adeboye, ya yi magana a game da rade-radin da ke yawo na cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta taso Yemi Osinbajo a gaba.

Malamin addinin na Kirista ya tabo wannan magana ne a jawabin da ya yi wajen taya murnar cikar wani cocin Darikar na RCCG da ke Yankin Gwarimpa a cikin Garin Abuja shekaru 20 da kafuwa.

Faston ya yi jawabi ne ba tare da tada jijiyon wuya ba inda ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasar zai tsallake duk wata gadar zare da aka shirya masa kamar yadda Vanguard ta rahoto jiya.

Malamin ya janyo wasu ayoyi daga surar Sulaimana mai tsarki cikin littafin Linjila inda yace Osinbajo ya zama mataimakin shugaban kasa ba tare da ya nema ba kamar yadda ya faru da Yahaduwa.

Shehin yake cewa wannan ya faru ne da Sarki Saul wanda ya mulki Yahaduwan Bani Isra’ila ba tare da ya nuna cewa ya na kwadayin mulki ba. Shi ma Yemi Osinbajo ya samu mulki ne a sama a 2015.

KU KARANTA: Babban Fasto Bakare ya bayyana abin da zai faru da Osinbajo

“Na yi addu’a tare da (Osinbajo) dazu nan, kuma Ubangiji ya sa na fahimci cewa wannan mutumi bai taba tunanin zai zama mataimakin shugaban kasa ba. Ba ‘Dan siyasa bane.” Inji Faston.

A jawabin Malamin, ya nuna cewa Osinbajo zai yi nasara domin kuwa Ubangiji ba zai kyale sa haka ba. “Idan Ubangiji ya nufi za ka zama wani, ko da mutane 100 ne a wurin, sai a kaudasu.”

Malamin ya kuma cewa: “Idan kai Ubangiji ya hara, shi zai rike a wuri.” A karshen jawabin na sa, Fasto Ezekiel Odeyemi a madadin Adeboye ya yi kira ga jama’a su rika gaskiya a ko da yaushe.

Fasto Enoch Adeboye ya yi wannan magana ne a karshen makon jiya a Ranar 6 ga Watan Oktoban 2019. Enoch Adeboye ya samu wakiltar babban Fasto Ezekiel Odeyemi na cocinsa ne a taron.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel