Wata dattijuwa mai shekaru 87 ta mutu ta bar jikoki 102 a Zamfara

Wata dattijuwa mai shekaru 87 ta mutu ta bar jikoki 102 a Zamfara

Hajiya Zainab Magaji, wata dattijuwa mai shekaru 87, ta mutu ta bar jikoki 102, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito ranar Litinin.

Dattijuwar, wacce ta haifi 'ya'ya hudu kacal a rayuwarta, ta mutu ta bar dumbin 'ya'yan jikoki da ba a kayyade yawansu ba.

Daga cikin 'ya'yan dattijuwar akwai Alhaji Ibrahim Dosara, shugaban gidan talabijin din 'Standard Voice' kuma tsohon mai bawa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Aldulazi Yari, shawara.

Hajiya Zainab ta rasu ranar Lahadi da safe bayan.

A cewar daya daga cikin 'ya'yanta, Alahji Ibrahim Dosara, Hajiya Zainab ta mutu ne a gidansa da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, bayan ta yi fama da takaitacciyar rashin lafiya, kuma an binne ta bisa tsarin addinin Islama a kauyen Dosara da ke karkashin karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

A wani labarin, Legit.ng ta wallafa cewa 'yan sanda a jihar Ogun sun kama wasu matsa biyu; Emmanuel Aro, mai shekaru 25, da Anu Olofinju, mai shekaru 25, bisa zarginsu da farke kabarin wata mata tare da cire kokon kan ta a wata makabarta da ke karamar hukumar Yewa ta Arewa.

DUBA WANNAN: Kasar Saudiyya ta bawa mace da namiji marasa aure 'yancin kama dakin Otal daya

Da yake tabbatar da kama matasan a ranar Lahadi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce an kama masu laifin ne biyo bayan korafin da wani mutum mai suna Amoo Bankole ya shigar a ofishin 'yan sanda da ke Eggua.

A cewar Oyeyemi, Bankole ya shigar da korafin cewa an ga matasan biyu na haka kabarin da aka binne mahaifiyarsa a 'ya watannin da suka gabata, kuma ya yi zargin cewa matasan na da wata mummunar manufa.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya bayyana cewa mutumin da ya shigar da korafin ya tabbatar da cewa kokon kan mahaifiyarsa ne aka samu tare da matasan.

Ya kara da cewa matasan sun amsa laifinsu tare da bayyana cewa zasu yi amfani da kokon kan matar ne domin yin tsafin samun kudi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel