Tsirarun mutane da ke zaune a jihohi 5 ne suka tattare arzikin Najeriya - Buhari

Tsirarun mutane da ke zaune a jihohi 5 ne suka tattare arzikin Najeriya - Buhari

A ranar Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa mafi yawan arzikin Najeriya na tattare a hannun wasu 'yan tsirarun mutane.

Shugaban kasar ya ce wadannan tsirarun mutane na zaune a jihohin Najeriya hudu zuwa biyar idan aka hada da babban birnin tarayya, Abuja.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a wurin bude wani taro a kan tattalin arzikin kasa da ake yi a Abuja.

Ya kara da cewa a yayin da masu arzikin ke zaune a jihohin Najeriya biyar, akwai ragowar 'yan Najeriya kusan miliyan 150 da ke zaman jiran samun ingantacciyar rayuwa a sauran jihohi.

Shugaba Buhari ya ce kafin jama'ar wata al'umma su zama masu rufin asiri, sai ya kasance mafi yawan jama'a na rayuwa cikin sukuni.

Ya ce gwamnatinsa ta fahimci cewa akwai bukatar 'yan Najeriya su zama masu rufin asiri, kuma hakan ne yasa gwamnatinsa ta dauki matakan rage rashin aiki da radadin talauci.

"Akwai banbanci tsakanin rufin asiri da arziki. Ba lalla suna nufin abu guda bane," a cewar shugaba Buhari.

DUBA WANNAN: Kotu za ta fara sauraron karar da aka shigar da Buhari a kan Osinbajo ranar Litinin

Buhari ya cigaba da cewa; "Arziki na nufin mallakar kudi masu yawa ko mallakar kadarori. Dole a samu rashin daidaito idan ya kasance wata kasa ta mayar da hankali wajen gina tattalin arzikinta domin kowa ya mallaki kudi da kadarori.

"Al'umma mai rufin asiri ita ce wacce mafi yawan jama'a ke rayuwa cikin sukuni, ba tare da fargabar abinci ko gama garin abubuwan more rayuwa ba.

"Akwai kimanin mutane miliyan 200 da ke zaune a jihohin Najeriya da birnin tarayya, Abuja.

"Mafi yawan arzikin Najeriya na hannun wasu 'yan tsirarun mutane da ke zaune a jihohin hudu ko biyar idan aka hada da birnin tarayya (FCT), Abuja. Wasu daga cikin irin wadannan tsirarun mutane na zaune a cikin dakin wannan taro."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel