Yanzu Yanzu: Gwamna Akeredolu ya sallami hadiminsa na musamman akan harkokin siyasa

Yanzu Yanzu: Gwamna Akeredolu ya sallami hadiminsa na musamman akan harkokin siyasa

- Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya sallami hadiminsa na musamman akan harkokin siyasa, Mista Augustine Pelemo

- Kwamishinan labarai na jihar, Mista Donald Ojogo ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba

- Gwamnan ya umurci Pelemo da ya mika kayayyakin gwamnati dake a hannunsa zuwa ga mataimakin shugaban ma’aikata

Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo a ranar Litinin, 7 ya watan Oktoba, ya sallami hadiminsa na musamman akan harkokin siyasa, Mista Augustine Pelemo.

A Wani jawabi daga Mista Donald Ojogo, kwamishinan labarai na jihar, a ranar Litinin a Akure, yace dakatarwar zai fara aiki nan take.

Ya yi bayanin cewa umurnin ya biyo bayan bukatar yin gyare-gyare a gwamnatin jihar.

KU KARANTA KUMA: Ka bai wa malaman Najeriya kwangilar addu’a idan kana son tsaron kasar – Shehu Sani ga Zulum

Ojogo yace gwamnan ya umurci Pelemo da ya mika kayayyakin gwamnati dake a hannunsa zuwa ga mataimakin shugaban ma’aikata sannan yayi masa fatan alkhairi a lamuransa na nan gaba.

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sallami dukkanin hadimansa guda 264 da ke wakiltan unguwanni da kananan hukumomi a jihar.

Hadiman da aka kora a ranar Laraba, 2 ga watan Oktoba, sun hada da hadimai na musamman guda 193, manyan hadimai na musamman guda 54 da hadimai na musamman guda 18, jaridar The Nation ta ruwaito.

Osarodion Ogie, sakataren jihar ya tabbatar da lamarin, inda yace sallaman na daga cikin shirin Gwamna Obaseki na yin garambawul a gwamnatin domin isar da aiki mai inganci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel