Wani a cikin Aso Villa ya na amfani da tsofaffin Mukarrabai a kan Yemi Osinbajo

Wani a cikin Aso Villa ya na amfani da tsofaffin Mukarrabai a kan Yemi Osinbajo

Wasu rade-radi na yawo cewa har ila yanzu, Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya na ta faman yaki da wasu masu rike da madafan iko a boye a cikin fadara Shugaban kasa.

Labarin da ke yawo yanzu shi ne akwai wani babba a cikin Aso Villa da ke yunkurin kara gumawa Mai girma Yemi Osinbajo matsala ta hanyar amfani da wasu manyan tsofaffin Jami'ain gwamnati.

Jaridar The Guardian ce ta fito da wani rahoto ne inda tace kawo yanzu ba a daina yakar mataimakin shugaban kasar ba domin a ruguza shirin da yake da shi na neman mulki a zaben 2023.

Majiyar Jaridar ta na cewa wadanda ke kitsa wannan danyen aiki a fadar shugaban kasar sun fito da wani sabon shiri na ganin yadda za su taka mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Daga cikin hanyar da ake bi a yanzu shi ne amfani da rundunar wasu Mukarraban gwamnati wanda su ka kunshi tsofaffin Hadiman Mataimakin shugaban kasar a baya, wajen taya su wannan yaki.

KU KARANTA: Yadda mu ka maka tsofaffin Gwamnoni 2 a gidan yari inji Osinbajo

Kamar yadda ake ta faman yadawa, daga cikin Tawagar da ake so ta bada gudumuwa wajen yakar Osinbajo akwai wani gawurtaccen ‘dan adawarsa a siyasa. Majiyar ba ta iya bayyana sunan wannan ba.

A cikin wadanda za a yi amfani da su wajen yakar Yemi Osinbajo a siyasance akwai Hadimansa da su ka rasa aikinsu a dalilin kokarin ragewa mataimakin shugaban kasar tasiri a fadar shugaban kasa.

The Guardian ta zargi shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa watau Malam Abba Kyari da kitsa duk wannan aiki. Wani da ake tunani da hannunsa a ciki shi ne wani tsohon gwamnan Legas.

Daga cikin wadanda Abba Kyari zai yi amfani da su a wajen wannan shiri akwai tsohon Shugaban hukumar DSS, Lawan Daura da kuma Ayo Oke wanda ya rike shugaban hukumar NIA ta kasa.

Wani wanda ya yi magana da jaridar yake cewa duk wadanda Abba Kyari da Babagana Kingibe su ke jawowa don su yaki Osinbajo marasa gaskiya ne. Osinbajo ya kuma taba wasunsu a baya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel