Da duminsa: GUdun kada tarihi ya maimaita kansa, an kulle makarantan gwamnatin Dapchi

Da duminsa: GUdun kada tarihi ya maimaita kansa, an kulle makarantan gwamnatin Dapchi

Kungiyar malamai da iyayen makarantar Daphi da kungiyar yaran Dapchi da aka sace sun yanke shawarar kulle makarantar sakandaren mata zalla dake Dapci, jihar Yobe saboda gudun kada tarihi ya maimaita kansa.

Za ku tuna cewa a ranar 19 ga Febrairu, 2018, yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sun sace yan mata 104 daga makarantar.

Majiya a makarantar ya bayyana cewa kungiyoyin sun yanke wannan shawara na kulle makarantar ne bisa ga rahoton tsaron da aka basu har sau uku.

Tabbatar da wannan labari, shugaban kungiyar iyayen yan matan Dapchi, Ajhaji Bashir Manzo, ya bayyana cewa kwamandan JTF na garin ya basu umurnin kwashe yaransu daga makarantar zuwa gidan sarki.

Yace: "Jiyan nan (Asabar) an kai hari fadar sarkin Jajere kuma yan ta'addan sun kona fadar. Saboda haka, mun yi tunanin halin yaran na cikin hadari. Mun gana kuma mun yanke shawarar mayar da si gida yau (Lahadi)."

"Mun yi ittifaki wajen yanke wannan shawara saboda rahoton leken asiri da aka samu ranar Asabar cewa an ga yan ta'addan a kauyen Sassawa."

"Harin da suka kai garin Babbangida ya yanke dukkan shakka, shiyasa shugabancin makarantan ta gana da kungiyar malamai da iyaye da jami'an tsaro kuma muka yarde cewa a kulle makarantar."

Manzo ya ce sun rubutawa shugabannin jami'an tsaro da ma'aikatar ilimi domin sanar da su kan wannan shawara.

Ya ce dalibai su koma gida har zuwa lokacin da ya bayyana cewa an samu isasshen tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel