Boko Haram sun far ma fadar sarki a wani sabon hari da suka kai Yobe

Boko Haram sun far ma fadar sarki a wani sabon hari da suka kai Yobe

Rahotanni sun kawo cewa a ranar Asabar yan ta’addan Boko Haram sun kona wani sashi na fadar Sarki a hedikwatar Babangida da ke karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.

Majiya sun ce yan ta'addan sun shiga garin ne inda kai tsaye suka tafi fadar sarkin bayan sarkin ya bar fadar awa biyu kafin shigowar yan ta’addan.

Saboda haka, cikin fushi sai yan ta’addan suka yanke shawaran kona wani sashi na fadar sannan suka tafi da motar masu tsaron sarkin kiran Hilux.

Wani mazaunin Babangida ya fada ma manema labarai cewa yan ta’addan sun kasance da niyyar kashe basaraken a manufarsu na ramuwar gayya.

Majiyin ya bayyana cewa basaraken a baya ya bada rahoton kwararru wanda yayi sanadiyyar kashe wasu yan Boko Haram a yankin shi wadanda suka shahara wajen garkuwa da mutane da kuma amsan kudin fansa.

Bayanai da aka samu har ila yau ya nuna cewa hari akan garin ya janyo tsoro a zukatan mazauna kauyen yayinda yawancin su da suka je kasuwa suka tsere don neman tsira.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa an janye dakarun sojoji daga Tarmuwa fiye da watanni biyu da suka gabata sakamakon dabaran rundunar soja na kafa manyan sansani a Operation Lafiya Dole.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram: An bai wa malamai 30 kwangilar addu'a a Saudiyya

Wani mazaunin kauyen mai suna Idris Adamu ya bayyana cewa sojoji sun zo daga Dapchi awa daya bayan harin.

Kauyen Tamuwa na a tsawon kilomita 53 daga Damaturu, babbar birnin jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel