Samar da aikin yi da daukar matasa aiki shine babban abunda gwamnatin tarayya ta sanya a gaba - Keyamo

Samar da aikin yi da daukar matasa aiki shine babban abunda gwamnatin tarayya ta sanya a gaba - Keyamo

Karamin ministan kwadago da diban ma'aikata, Festus Keyamo ya bayyana cewa samar da aikin yi ga matasa ya kasance daga cikin manyan manufofin da ke tattare da ajandar Next Level, na Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar matasan Afrika wato "Pan African Youth Union" a karkashin jagorancin Mista Niyi Oladele John, a lokacin da suka ka masa ziyarar bangirma.

Yace matsalar rashin tsaro ya mamaye fadin nahiyar Afrika sannan kuma cewa lamarin na dada tabarbarewa ne sakamakon rashin samar da ayyukan yi ga matasa.

“Tunanin ma’aikatar kwadago da kuma wannan gwamnatin shine samar da aiki ga matasa ya kasance kan gaba a ajendarmu kuma wannan ne dalilin da yasa Shugaban kasa ya yanke shawaran karfafa ma’aikatar da hukumominta.

"Akwai shirye-shirye da dama a kakashi ma'aikatar da hukumominta wadanda musamman aka kafa su domin tallafawa matasanmu ta anya tabbata da cewa sun koyi sana'o'i da zai basu dama dogao da kansu," inji shi.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Rikicin gona yayi sanadiyar kashe mutum 3 tare da jikkata 8 a Nasarawa

Ya kara da cewar akwai bukatar kungiyar matasan ta samar da bayanan matasa kwararu wadanda gwamnatin Tarayya zata iya amfani dasu wajen iya gano wadanda zata iya horaswa, inda ya kara da cewa ta hakan ne gwamnatin zata cimma manufofinta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel