Hukumar NYSC ta tsawaita hidimar masu bautar kasa 52 a Kano

Hukumar NYSC ta tsawaita hidimar masu bautar kasa 52 a Kano

Hukumar NYSC mai kula da masu yi wa kasa hidima, ta yanke hukuncin tsawaita wa'adin yi wa kasa bauta kan wasu masu hidimtawa kasar 52 a jihar Kano.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito cewa, hukumar NYSC ta zartar da matakin hakan ne da zummar hukunta masu bautar kasar a sanadiyar laifukan da suka aikata na yi wa wuraren da aka tura su hidima 'a sha ruwan tsintsaye'.

Shugaban hukumar NYSC reshen jihar Kano, Ladan Baba, shi ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Kanon Dabo a ranar Juma'ar da ta gabata.

Alhaji Baba ya ce cikin wadanda hukumar ta zartar da hukunci a kansu, akwai 26 da a dole sai sun maimata shekara guda cir na yi wa kasa hidima, a sakamakon kauracewa wuraren da aka tura su bauta na tsawon fiye da watannin uku.

Ya ce ragowar 26 da hukumar ta tsawaita wa'adin bautar su da kimanin wata daya zuwa watannin uku, ya bayu ne a sanadiyar 'a sha ruwan tsintsaye' da suka rinka yi na tafiye-tafiye ba tare da neman izini ba.

KARANTA KUMA: Kotun zabe ta tabbatar da nasarar gwamna Ortom na Binuwai

Ya kara da cewa, masu bautar kasa 1,942 da suka kunshi maza 1,220 da mata 719, sun kammala aikin hidimar su a jihar Kano bayan shafe tsawon shekara guda, wanda kundin tsarin mulkin kasa ya rataya a wuyan duk wani dan kasar nan da ya kammala karatun digiri ko kuma babbar difloma kuma bai haura shekaru 30 na haihuwa ba.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel