Kotun zabe ta tabbatar da nasarar gwamna Ortom na Binuwai

Kotun zabe ta tabbatar da nasarar gwamna Ortom na Binuwai

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Benuwe da ke zamanta a birnin Makurdi, a ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, ta tabbatar da nasarar gwamna Samuel Ortom kamar yadda rahotanni na jaridar The Nation suka ruwaito.

Tun a baya an ruwaito cewa, kotun za ta yanke hukunci kan shari'ar da ke tsakanin gwamna Ortom na jam'iyyar PDP da kuma abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Emmanuel Jime.

Mista Jime wanda ya yi takarar gwamnan jihar ya kalubalanci sakamakon zaben da aka gudanar watanni kadan da suka gabata bayan da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ta tabbatar da nasarar gwamnan mai ci na PDP.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Jime ya kalubalanci nasarar gwamna Ortoma da cewa zaben da ya gudana bai tsarkaka daga magudi ba da kuma saba wa ka'idodi na shari'a da kundin tsarin mulki ya yi tanadi.

Haka zalika a ranar Larabar makon da ya gabata ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a jihar Kano, ta yanke hukunci kan shari'ar da ke tsakanin gwamnan jihar mai ci da abokin hamayyarsa.

KARANTA KUMA: Riko da addini ya sa na gina Masallaci da Coci a dakin karatu na - Obasanjo

A shari'ar da kotun ta zartar kan zaben Kano na ranar 9 ga watan Maris, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, mai inkiyar 'Abba-Gida-Gida', sun fafata a gaban kotun bisa jagorancin babbar Alkaliya, Halima Shamaki.

Mai shari'a Shamaki ta ce, ta yi watsi da karar da dan takarar na jam'iyyar PDP ya shigar a sanadiyar yadda ya gaza gamsar da kotun cewa an tafka magudi a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Maris, lamarin da ta ce Gwamna Ganduje shi ne zababben gwamnan jihar Kano a zaben da ya gudana.

Haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kotun da ke sauraron karar zaben gwamna a jihar Bauchi, ta jaddada nasarar Gwamna Bala Mohammed na jam'iyya mai ci a jihar ta PDP.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel