Zaben 2019 alama ce ta bunkasar dimokuradiyya a Najeriya - Buhari

Zaben 2019 alama ce ta bunkasar dimokuradiyya a Najeriya - Buhari

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, a ranar Litinin 7 ga watan Oktoban 2019, ya fayyace dalilai da suka tabbatar da cewa dimokuradiyyar kasar na ci gaba da bunkasa tare da taka mataki na inganci.

Shugaban kasar kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito ya bayyana cewa, yadda babban zaben kasa na 2019 ya gudana salin-alin cikin zaman lafiya da aminci, manuniya ce da ke nuni da cewa dimokuradiyyar kasar na ci gaba da bunkasa.

Furucin shugaban kasar ya zo ne a birnin Abuja yayin bude taron tattalin arzikin Najeriya karo na 25 mai lakanin "Nigeria 2050: Shifting Gears".

Ya kara da cewa, hakkin da fusatattun 'yan takara ke nema ta hanyar dokoki na shari'a wajen raba gardamar sakamakon zabe, wata babbar alama ce da ke tabbatar da bunkasar dimokuradiyya a kasar.

Haka kuma shugaba Buhari ya ce irin yadda mafiya akasarin 'yan takara na zaben da ya gabata suka karkatar da akalar su ta muhimmanci a kan habaka tattalin arzikin kasa, wata hujja mai zaman kanta ta bunkasar dimokuradiyya, wadda ake yi wa kirari da rigar 'yanci.

Baya ga haka shugaba Buhari ya ce yaye kangi na talauci, inganta tsaro, yaki da rashawa da kuma samar da ayyukan yi gami da inganta jin dadin rayuwar al'ummar kasar nan, za su ci gaba da kasance wa a mafi kololuwar mataki na muhimmanci da jam'iyyarsa ta APC ta sanya a gaba.

KARANTA KUMA: Yarbawa ne za su karbi mulkin Najeriya a 2023 - Olayiwola

A wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Darakta Janar na hukumar kula da birnin Kano da kewaye, Abdullahi Ramat, ya fadi adadin dukiya da gwamnatin jihar ke batar wa a kowane wata domin kula da injinan samar da wutar lantarki domin haskaka titunan jihar.

Alhaji Ramat ya ce gwamnatin jihar Kano karkashin jagoranci gwamna Abdullahi Umar Ganduje tana batar da naira miliyan 200 a kowane wata wajen kula da injinan samar da wutar lantarki 149 domin haskaka titunan birnin Kano.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel