Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Rikicin gona yayi sanadiyar kashe mutum 3 tare da jikkata 8 a Nasarawa

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Rikicin gona yayi sanadiyar kashe mutum 3 tare da jikkata 8 a Nasarawa

Rahotanni sun kawo cewa an kashe mutane uku sannan aka jikkata wasu takwas a lokacin wani rikici kan gona a yankin Mada na Agidi da ke karamar hukumar Nasarawa Eggon a jihar Nasarawa.

An tattaro cewa rikicin ya afku ne tsananin bangarori biyu, Agbashuru da Ikkah-Wangibi na kabilar Eggon.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa yan uwan biyu na ta ikirarin mallakar gonar shinkafar, yayinda lamarin ke a kotu.

Rikicin ya fara ne lokacin da su duka biyun da ke ikirarin mallakar gonar suka je chan sannan suka fara girbe shinkafa. An tattaro cewa rikicin ya haddasa mutane tserewa daga gidajensu.

Kakakin yan sanda na jihar, ASP Ramhan Nansel ya tabbatar da lamarin, inda ya kara da cewa Wani Nasiru Yakubu na samun kulawar likita a asibitin Eggon.

Shugaban karamar hukumar Nasarawa Eggon, Mista Danladi Idris yace an zuba jami’an tsaro sannan cewa zaman lafiya ya dawo a yankin.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sake sakin mutane 15 da suka yi garkuwa da su a Katsina

Gwamna Abdullahi Sule, wanda ya ziyarci yankin yace: “Ina don mutane su san cewa za a tsamo duk wanda ke da hannua haddasa rikicin.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel