Yan bindiga sun sake sakin mutane 15 da suka yi garkuwa da su a Katsina

Yan bindiga sun sake sakin mutane 15 da suka yi garkuwa da su a Katsina

Yan bindiga sun sake sakin wani rukuni na mutane 15 da suka yi garkuwa da su a jihar Katsina daga cikin yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar.

Mutanen 15 sun kasance a sansanin masu garkuwa da mutanen dake dajin Dansadau a Zamfara, na tsawon kwanaki 44.

Wadanda aka saki sun hada da mata 13, dan shekara daya, da wani jinjiri da aka haifa kwana daya kafin sakin nasu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa da fari an saki mutane 30 da aka yi garkuwa dasu duk a cikin yarjejeniyar zaman lafiya.

Gwamnatin jihar ta tattauna tare da yan bindigan domin kawo karshen hare-haren da ake kaiwa kananan hukumomi takwas da ke jihar.

A Wani jawabi dauke da sa hannun darakta janar na labarai, Mista Abdu Labaran, yace an mika mutanen ya Gwamna Aminu Masari a ranar Lahadi a Katsina.

A cewarsa mutanen da aka saki sun yi ikirarin dandana kudarsu a hannun yan bindigan.

Da take bayanin halin da ta riski kanta, matar da ta haihu, Murja ta bayyana cewa an ajiye su a wani sansani dake dauke da mutane 150 da aka yi garkuwa dasu, amma kadan kadan sai suka rage su 13.

Tace basu taba tunanin za a sake su ba domin wadanda suka yi garkuwa dasu kan kasance cikin mummunan yanayi a koda yaushe, sannan suna barazanar kashe su tunda yan uwansu sun ki biyan kudi domin a sake su.

KU KARANTA KUMA: Kaduna: Masu garkuwa da mutane sun nemi fansar N10m kan kowace Yarinya

A cewar jawabin, gwamnan ya kaddamar da cewa mutanen 15 sune na karshe da aka San suna tsare.

Ya bayyana cewa a yanzu da aka saki dukkanin mutanen na jihar, “rukunin gaba na yarjejeniyar zaman lafiyan a Katsina shine yan bindigan su ajiye makamansu."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel