N200m gwamnati ta ke batar wa a kowane wata domin samar da haske a titunan birnin Kano

N200m gwamnati ta ke batar wa a kowane wata domin samar da haske a titunan birnin Kano

Darakta Janar na hukumar kula da birnin Kano da kewaye, Abdullahi Ramat, ya fadi adadin dukiya da gwamnatin jihar ke batar wa a kowane wata domin kula da injinan samar da wutar lantarki domin haskaka titunan jihar.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, Alhaji Ramat ya ce gwamnatin jihar Kano na batar da naira miliyan 200 a kowane wata domin kula da injinan samar da wutar lantarki 149 wajen haskaka titunan birnin Kano.

A wata hirarsa da manema labarai na gidan radiyon muryar jama'a da ke birnin Kanon Dabo, Alhaji Ramat ya ce a yanzu gwamnatin jihar na ci gaba da kwankwashe-kwanshen neman hanyoyin samun rangwami na kudaden da ta ke batar wa wajen kula da fitilun titunan birnin Kano.

KARANTA KUMA: Gwamna Matawalle ya nada sakataren yada labarai na jihar Zamfara

A wani rahoton na daban da muka kalato daga jaridar BBC Hausa, mun samu cewa, bayanai da ke fitowa daga garin Kwanar Dangora da ke kan hanyar Zaria zuwa Kano na cewa direbobin manyan motoci sun rufe hanyar ruf, al'amarin da ya janyo tsayawar sufuri a kan hanyar cik.

An dai ce al'amarin ya faru ne bayan da wani soja ya harbe wani direban babbar motar dakon kaya ta Dangote sakamakon tsayar da shi da suka yi a shingensu amma kuma ya yi masu kunnen uwar shegu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel