Masari: Akwai masu kokarin kawowa tafiyar APC da Gwamnatina matsala daga Abuja

Masari: Akwai masu kokarin kawowa tafiyar APC da Gwamnatina matsala daga Abuja

Gwamna jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya na zargin cewa akwai wasu ‘Yan siyasar Katsina da ke Abuja da su ke amfani da karfin gwamnatin tarayya domin kawowa APC matsala a gida.

Daily Trust ta rahoto Mai girma gwamnan a wajen wani taro ya na cewa wadannan ‘Yan APC da ke buga siyasarsu a waje sun a kokarin jefa jam’iyya da gwamnatinsa cikin twani hali a Katsina.

Aminu Bello Masari ya yi wannan bayani ne lokacin da ya gana da duk jagorori shugabannin jam’iyyar APC mai mulki daga kananun hukumomi 34 na jihar Katsina a karshen makon jiya.

Rt. Hon. Aminu Masari yake cewa jam’iyyar ta na bukatar wani irin garambawul domin abubuwa su mika. Har ila yau, gwamnan ya bayyana cewa rashin bin doka na iya kawo karshen APC.

“An kai bangaren APC na jihar Katsina da gwamnatina kara har gaban kotu sau biyu wanda doka ta tanadarwa duk wanda ya yi wa jam’iyya wannan a fatattake. Sau biyu ana kai mu kotun koli.”

KU KARANTA: Buba Galadima yace Buhari ya fito a mutum bayan ya samu mulki

Gwamnan ya cigaba da banbami inda ya fadi abin da ke faruwa: “Ana amfani da kudin gwamnatin tarayya wajen yakarmu, kuma har yanzu da su ake amfani, mun san abubuwan da ke faruwa.”

“Mu na nan, wadanda su ka rasa zaben fitar da gwani a 2015 har yau ba su shigo cikin Katsina ba. Ba za mu kyalesu, su kawo mana matslaa a siyarsarmu da mulkin mu ba.” Inji gwamnan jihar.

“Wadannan mutane ne su ka hada kai da PDP a kotun karar zabe domin a rusa nasarar mu. Kuma su ne su ka buga katin shaidar jam’iyya miliyan biyu domin kawo rikici a zaben fitar da gwani.”

Wani Jagoran APC a jihar, Bala Abubakar, ya tabbatar da haka inda yace za su fatattaki wadannan ‘yan siyasa daga APC. “Za su iya zama ‘Yan APC a Abuja, amma ba a Katsina ba.” Inji Bala.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel