Mulki ya nunawa kowa ainihin fuskar Shugaba Buhari Inji Buba Galadima

Mulki ya nunawa kowa ainihin fuskar Shugaba Buhari Inji Buba Galadima

Dattijon ‘dan siyasar nan na Arewa watau Injiniya Buba Galadima, ya bayyana cewa mulki ya tonawa shugaban kasa Muhammadu Buhari. Galadima yace wannan abin kunya ne ga shugaban.

Buba Galadima ya bayyana wannan ne a wata hira da ya yi a Jaridar New Telegraph inda yace da Buhari ya tsaya kan manufofin da aka san shi da su a baya, da Najeriya ta cigaba a mulkinsa.

Injiniyan yake cewa Buhari ya samu abin da yake so na mulkin Najeriya bayan da ya hada kai da sauran bangarorin kasar. Sai dai a cewarasa, bayan Buhari ya samu mulki sai ya fito a mutum.

Galadima yace: “Shi Buhari ya san abin da ya kawo sa mulki, ya san irin sadaukarwar da wasunmu su ka yi domin ganin ya zama shugaban kasa, amma ya na samun mulki ya fatattake mu.”

Buba Galadima yake cewa an yi watsi da duk wadanda su ka yi wa Buhari gwagwarmaya har ta kai aka tsare su da sunan sun ci amanar kasa. Galadima ya rike Sakatare na jam’iyyar CPC a 2011.

KU KARANTA: Za a saurari karar da aka kai shugaba Buhari a gaban kotu

“Da mun bi tsarin da mu ka shirya a 2002, da yanzu Najeriya ta zama irin su kasar Indonesiya, Maleshiya, Singafo, Indiya da sauran kasashen da su ka cigaba.” Inji babban Jigon adawar kasar.

"Mun yi wa Buhari yakin shekara da shekaru, amma wannan bai sa ya zama shugaban kasa ba sai da ya tsallaka ya hadu da sauran yankunan Najeriya. Nan ya ci zabe, kuma aka gane halinsa."

A game da zargin PDP da kashe kasar nan da Buhari ya saba, Galadima yace “Mu yarda cewa da gaske ne an kashe kasar nan. Meyasa aka zabe shi? Ba an zabe sa ba ne domin ya kawo mafita?”

Galadima ya tike da: “Wannan ba hujja ba ce da za a rika daura laifi a kan gwamnatocin baya. Abin ya na bani dariya. A cikinsu, wanene bai cikin gwamnatin PDP, har shugaban kasan kansa.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel