Najeriya ba za ta taba arziki idan Jihohi ba su da karfi ba ba – Osinbajo

Najeriya ba za ta taba arziki idan Jihohi ba su da karfi ba ba – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa Najeriya za ta kara karfi idan har jihohi su ka iya kara kokari wajen tatso kudin shiga tare da samun iko a kan arzikinsu.

Yemi Osinbajo ya yi wannan bayani ne da ya ke jawabinsa na laccar bikin samun ‘yancin kai a wata Unguwa da ke Yankin Ikoyi a jihar Legas. An shirya laccar ne a Ranar 4 ga Oktoban 2019.

Kamar yadda Jaridar The Nation ta rahoto a Ranar Juma’ar, Farfesa Osinbajo ya yi kira da tarin Kabilu da dinbin jama’an da ake da su a Najeriya su hada-kai domin a ciyar da kasar zuwa gaba.

“Za a cin ma wannan buri ne idan jihohi su ka kara karfin samu da iko da arzikinsu. Babban sauyin da za a kawo a Najeriya shi ne samar da dukiya wanda zai raba mutane daga talauci.”

KU KARANTA: Kotu za ta fara sauraron karar da aka shigar da Buhari

Osinbajo ya kara da: “Najeriya ba za ta taba arziki ba idan jihohin da su ka hadu su ka hada kasar ba su da arziki. Halin da Najeriya ta ke ciki ya danganta ne da halin da jihohinta su ke ciki.”

Mataimakin shugaban na Najeriya yake cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta na son ganin jihohi sun kara tashi a tsaye. Yaki da talauci dai ya na cikin manyan muradun gwamnatin Buhari.

A game da yakin da cin hanci da rashawa, Osinbajo yace gwamnatin su za ta cigaba da yakar rashin gaskiya. “Yanzu tsofaffin gwamnoni biyu su na gidan yari bayan kotu ta same su da laifi.”

“Akwai nawa a tsarinmu amma mun kai ga wannan nasara. Abin da na ke so a sani shi ne masu laifin nan su na kokarin yakarmu. Su na kokarin nuna cewa kowa ma a kasar maras gaskiya ne.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel