Kotu za ta fara sauraron karar da aka shigar da Buhari a kan Osinbajo ranar Litinin

Kotu za ta fara sauraron karar da aka shigar da Buhari a kan Osinbajo ranar Litinin

A ranar Litinin, 07 ga watan Satumba, ne wata kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a jihar Legas za ta fara sauraron karar da wani lauya mazaunin jihar Legas, Inihebe Effiong, ya shigar da shugaba Buhari a kan kin mika mulki ga mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, yayin da ya yi bulaguro zuwa kasar Ingila daga ranar 25 ga watan Afrilu zuwa 5 ga watan Mayu, 2019.

An saka sunan ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN), a cikin wadanda ake kara.

A cikin takardar kara mai lamba FHC/L/CS/763/2019 da Effiong ya shigar, ya nemi kotun ta yi duba na tsanaki bisa dogaro da sashe na 145 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya wajen zartar da hukunci a kan kin mika ragamar mulki ga Osinbajo da Buhari ya yi a lokacin da ya bar Najeriya na takaitaccen lokaci.

Doka ta bukaci cewa shugaban kasa zai rubuta wasika zuwa ga shugaban majalisar dattijai da kuma shugaban majalisar wakilai domin sanar da su cewa mataimakinsa zai cigaba da gudanar da al'amuran gwamnati yayin da baya nan, dokar da lauya Effiong ya zargi shugaba Buhari da yi wa 'karen tsaye'.

Kazalika, lauyan ya bukaci kotun ta bayyana dacewa ko sabanin hakan a kan ikon da shugaban kasa ke da shi na cigaba da sarrafa akalar al'amuran gwamnati a yayin da ya bar kasa ko yana wata kasar ketare.

DUBA WANNAN: A cikin kwanaki 45, na cimma abinda ba zai yiwu ba a cikin shekaru 7 - Pantami

Sai dai, a hujjar da suka gabatar domin kare kansu, Buhari da Malami sun bayyana cewa doka ta bawa shugaban kasa wa'adin kwanaki 21 domin ya rubuta irin wasikar da lauyan ya ambata ga shugaban majalisar dattijai da wakilai.

Kazalika, shugaba Buhari ya bayyana cewa ya yi bulaguro ne na tsawon kwanaki 9 kacal, tare da bayyana cewa bai zarce wa'adin kwanaki 21 da doka ta diba masa ba.

Buhari ya musanta zargin lauya Effiong a kan cewa ya shafe kwanaki 9 a kasar Ingila domin huta wa.

Lauyoyin Buhari sun musanta tare da kalubalantar lauya Effiong ya gabatar da wata hujja da ke nuna cewa shugaba Buhari ya ziyarci kasar Ingila ne domin huta wa tare da rokon kotun ta yi watsi da karar da lauyan ya shigar.

Za a fara fafata wa a gaban kotun da mai shari'a Jastis A. O Faji ke jagoranta ranar Litinin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel