Luguden wuta: Dakarun NAF sun kashe mayakan ISWAP masu yawa a maboyarsu

Luguden wuta: Dakarun NAF sun kashe mayakan ISWAP masu yawa a maboyarsu

Wani jirgin yakin rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ya yi luguden wuta tare da kashe mayakan kungiyar ISWAP (Islamic State for West African Province) da dama yayin wani hari ta sararin samaniya da dakarun rundunar suka kai maboyar 'yan ta'addar a Kirta Wulgo da ke daura da tekun Chad a jihar Borno.

NAF ta ce dakarunta sun kai hari sansanin ne bayan samun sahihan bayanan cewa daga wurin ne mayakan kungiyar ISWAP ke tsara hare-haren da suke kai wa rundunar soji.

A jawabin da Ibikunle Daramola, darektan yada labarai da hulda da jama'a na rundunar soji ya fitar, ya ce luguduen wutar da jirgin yakin NAF ya yi a sansanin ya yi sanadiyar lalata wuraren da mayakan ke fake wa.

"Hare-haren da rundunar NAF ke kai wa a kan birbishin mayakan kungiyar ISWAP na cigaba da yin tasiri a yakin da dakarun soji ke yi da 'yan ta'adda da aiyukan ta'addanci a yankin arewa maso gabas. NAF ta kara samun nasarar lalata wani sansanin mayakan ISWAP da ke Kirta Wulgo mai makwabtaka da tekun Chadi a jihar Borno.

"Dakarun ATF a karkashin rundunar atisayen Lafiya Dole, sune suka kai hari sansanin ranar Asabar bayan kammala tattara bayanan sirri a kan sansanin da mayakan ke amfani da shi domin tsara wa da shirya hare-haren da suke kai rundunar sojoji," a cewar sa.

DUBA WANNAN: Dakarun NAF sun yi luguden wuta a Kaduna, sun kashe 'yan bindiga 10

A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin jihar Borno ta saki a kalla tsofin mayakan kungiyar Boko Haram 132 ranar Lahadi domin su koma cikin jama'a su cigaba da rayuwa bayan kammala basu horo.

Kwamishiniyar harkokin mata da walwalar jama'a a jihar Borno, Hajiya Zuwaira Gambo, ita ce ta sanar da hakan yayin bikin sakin tsofin mayakan Boko Haram da aka yi a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ta ce an bawa tsofin mayakan horon ne domin samun sana'o'in da zasu yi domin su dogara da kansu bayan sun koma rayuwa a cikin sauran jama'a, kamar sauran gama garin mutnane.

Zuwaira ta ce an damka tsofin mayakan a hannun danginsu da jami'an kananan hukumomin da suka fito bayan an kammala basu horon gyaran halayya da tunani da kuma koya musu sana'o'i a wata cibiya da ke Bulunkutu.

Ta kara da cewa an bawa tsofin mayakan kekunan dinki, kayan aski, akwakun gyaran takalma, kudade da kuma sauran tallafin kayan amfani bayan an basu horo na tsawon shekara guda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel