Gwamnatin jihar Borno ta saki tsofin 'yan Boko Haram 132

Gwamnatin jihar Borno ta saki tsofin 'yan Boko Haram 132

A kalla tsofin mayakan kungiyar Boko Haram 132 gwamnatin jihar Borno ta saki ranar Lahadi domin su koma cikin jama'a su cigaba da rayuwa bayan kammala basu horo.

Kwamishiniyar harkokin mata da walwalar jama'a a jihar Borno, Hajiya Zuwaira Gambo, ita ce ta sanar da hakan yayin bikin sakin tsofin mayakan Boko Haram da aka yi a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ta ce an bawa tsofin mayakan horon ne domin samun sana'o'in da zasu yi domin su dogara da kansu bayan sun koma rayuwa a cikin sauran jama'a, kamar sauran gama garin mutnane.

Zuwaira ta ce an damka tsofin mayakan a hannun danginsu da jami'an kananan hukumomin da suka fito bayan an kammala basu horon gyaran halayya da tunani da kuma koya musu sana'o'i a wata cibiya da ke Bulunkutu.

Ta kara da cewa an bawa tsofin mayakan kekunan dinki, kayan aski, akwakun gyaran takalma, kudade da kuma sauran tallafin kayan amfani bayan an basu horo na tsawon shekara guda.

DUBA WANNAN: Jami'an kwastam sun kama buhunhunan tabar wiwi da darajarsu ya kai miliyan N169

Bashir Ahmed, daya daga cikin wadanda aka saki, ya gode wa gwamnatin jihar Borno bisa basu damar sake yin rayuwa kamar sauran mutane.

"Mu na masu matukar godiya ga gwamnatin jihar Borno da sauran kungiyoyin kasa da kasa da ke taimakon 'yan gudun hijira da kuma sauran kungiyoyin jin kai.

"Mun ji dadin wannan shiri na bayar da horon gyaran halayya da koyar da sana'o'i ga tsofin mayaka domin su zamo 'yan kasa nagari, masu amfani," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel