Dakarun NAF sun yi luguden wuta a Kaduna, sun kashe 'yan bindiga 10

Dakarun NAF sun yi luguden wuta a Kaduna, sun kashe 'yan bindiga 10

Rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF) ta ce dakarunta na rundunar atisayen HADARIN DAJI (OPHD) sun kashe a kalla 'yan bindiga 10 yayin luguden wuta a wani jeji da ke kusa da Birnin Gwari da tsaunin Janko a jihar Kaduna.

Ibikunle Daramola, darektan yada labarai da hulda da jama'a na NAF, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, inda ya bayyana cewa sojojin sun yi luguden wuta a sansanin 'yan bindigar ne ranar Asabar.

"Dakarun rundunar OPHD, bayan samun umarni daga hedikwatar NAF, sun kai hari wasu sansanin 'yan bindiga da aka tabbatar da cewa 'yan bindigar da suka ki tuba na cigaba da buya a sansanin da ke yankin jihar Kaduna.

"An kai hari sansanin ne biyo bayan harin da 'yan bindiga suka kai a garin Sunke da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara da kuma ciga da hijirar da 'yan bindiga ke yi daga jihar Zamfara zuwa Birnin Gwari, yankin jihar Kaduna," a cewarsa.

Mista Daramola ya bayyana cewa wasu jiragen yakin rundunar NAF guda biyu ne suka kai harin bayan an tabbatar da ganin 'yan bindiga a sansanin da aka yi wa luguden wuta daga sararin samaniya.

DUBA WANNAN: A cikin kwanaki 45, na cimma abinda ba zai yiwu ba a cikin shekaru 7

Kazalika, ya ce dakarun rundunar OPHD sun bi wasu 'yan bindigar zuwa tsaunin Janko tare da kashe su a wurin.

Daramola ya ce dakarun rundunar OPHD sun kara matsa lamba wajen kai hare-hare a kan sannsanin 'yan bindigar domin tabbatar da dorewar zaman lafiyar da aka fara samu a yaki da aiyukan ta'addanci a yankin arewa maso yamma.

A cewar Daramola, dakarun rundunar atisayen OPHD zasu cigaba da sintiri da shawagi a yankin domin tabbatar da cewa 'yan bindigar basu samu sukunin sukurkuta zaman lafiyar da ya fara dawowa yankin ba, tare da yin kira ga duk masu hannu a cikin aiyukan ta'addanci a yankin da su tuba, su zubar da makamansu ko kuma su fuskanci fushin rundunar soji da sauran jami'an tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel