Harin ‘yan-bindiga: Gwamnatin Zamfara ta kira wata ganawar gaggawa domin tattauna matsalar

Harin ‘yan-bindiga: Gwamnatin Zamfara ta kira wata ganawar gaggawa domin tattauna matsalar

Gwamnatin jihar Zamfara ta kira wani zama na musamman dangane da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Sunke dake karamar hukumar Anka inda aka kashe sojoji 9.

Wannan zaman dai gwamnatin Zamfara ta shirya shi ne da shuwagabannin Fulani domin tattaunawa a kan wannan mummunan harin da aka kai kwanan nan.

KU KARANTA:Zargin cin-hanci: Mu hadu a kotu, tsohon gwamnan jihar Bauchi ya maka gwamnatin jihar kara

Babban mai ba gwamna Zamfara shawara a kan lamuran tsaro, Alhaji Abubakar Dauran ya shaidawa manema labarai a Gusau ranar Asabar cewa an shirya zaman ne domin kare sake aukuwar irin hakan a nan gaba.

Sai dai kuma bai fadi lokaci da za a gudanar da zaman ba. Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ta tattaro mana bayanan cewa wannan harin shi ne hari na farko tun bayan da gwamnatin Zamfara ta yi zaman sulhu da ‘yan bindigan.

Dauran ya tabbatar mana da cewa harin wanda ya auku a ranar Alhamis 3 ga Oktoba ya yi sanadiyar mutuwar sojoji 9 tare da raunata wasu da dama wadanda a yanzu haka suke kwance a asibitin FMC, Gusau.

A cewar hadimin gwamnan, wadanda suka kai wannan harin ba ‘yan asalin jihar Zamfara ba ne, mutanen jihar Neja ne.

“Tun bayan da gwamnatinmu tayi zaman sulhu da ‘yan bindiga a jihar nan, mun samu zaman lafiya da kwanciyar hankali saboda dukkanin ‘yan bindiga sun tuba daga laifukansu.

“Ina da tabbacin cewa wadanda suka kai wannan harin ba ‘yan asalin jihar Zamfara ba ne. Jim kadan bayan an kai harin mun zanta da shuwagabannin Fulani inda suka bamu tabbacin cewa ba su da hannu cikin harin.” Inji Dauran.

https://www.vanguardngr.com/2019/10/zamfara-govt-summons-emergency-meeting-over-fulani-attacks/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel