Gwamna Matawalle ya nada sakataren yada labarai na jihar Zamfara

Gwamna Matawalle ya nada sakataren yada labarai na jihar Zamfara

- Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya yi nadin babban mukamin a fadar gwamnatinsa

- Gwamna Matawalle ya nada Jamilu Iliyasu Birnin Magaji a matsayin sakataren sadarwa da yada labarai na fadar gwamnatin Zamfara

- Alhaji Birnin Magaji ya sha alwashin sadaukar da kai gami da jajircewa tare yin aiki tukuru iyaka bakin kokari

Mun samu rahoton cewa, gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara, ya nada Alhaji Jamilu Iliyasu Birnin-Magaji, a matsayin babban sakataren sadarwa da yada labarai na fadar gwamnatinsa da ke birnin Gusau.

Sanarwar da ta gabata a ranar Lahadi na kunshe cikin wata rubutacciyar wasika da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Bala Bello.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, Alhaji Birnin-Magaji ya kasance tsohon sakataren kungiyar 'yan jarida reshen jihar Zamfara gabanin wannan mukami da ya samu.

Haka kuma gabanin wannan nadi, sabon sakataren sadarwa na gwamnati Zamfara ya kasance tsohon mai watsa rahotanni a gidajen radiyo da talabijin na jihar kuma bataskaren fadar gwamnatin da ke birnin Gusau.

Da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Lahadi, Alhaji Birnin Magaji ya sha alwashin sadaukar da kai gami da jajircewa tare da yin aiki tukuru wajen sauke nauyin al'ummar jihar da gwamna Matawalle ya rataya masa a wuya.

KARANTA KUMA: Samar da aikin yi da daukar matasa aiki shine babban abunda gwamnatin tarayya ta sanya a gaba - Keyamo

Bayan godiya da yabo ga gwamna Matawalle, sabon sakataren yada labarai na jihar ya kuma sha alwashin sanar da al'ummar Zamfara dukkanin wasu ayyuka da shirye-shirye na gwamnatin jihar da manufa ta fidda ita zuwa tudun tsira.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel